Ba zamu yarda Tinubu ya dauki Musulmi matsayin abokin tafiyarsa ba, Babachir Lawal

Ba zamu yarda Tinubu ya dauki Musulmi matsayin abokin tafiyarsa ba, Babachir Lawal

  • Babachir Lawal ya yi kira ga jam'iyyar APC su zabi Kirista ya zama mataimakin Tinubu a zaben 2023
  • Tsohon sakataren gwamnatin yace Kiristoci ba zasu taba yarda a zabi Musulmi ya zama abokin tafiya ba
  • Hukumar INEC ta baiwa Tinubu da Atiku mako guda su mika sunayen abokan tafiyarsu

Abuja - Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa ba zai yiwu Tinubu ya dauki wani Musulmi matsayin mataimakinsa ba a zaben 2023.

Babachir ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da Seun Okinbaloye na ChannelsTV.

Ya ce sam ba zai yiwu wani yayi tunanin tikitin Musulmi da Musulmi ba dubi ga yadda lamarin siyasar Najeriya yake.

Yace:

"Za ku iya samun yan takara masu kyau amma idan baku ci zabe ba, bacin lokaci ne. Saboda haka mu sani cewa duk wanda aka zaba mataimaki zai taimaka wajen nasara a zabe."

Kara karanta wannan

Bamu yarda Musulmi da Musulmi su zama Shugaba da mataimaki ba: Kungiyar CAN

"Kan Shawarar tikitin Musulmi-Musulmi, cikin Kiristoci nike rayuwa kuma na san ba zasu yarda da lamarin nan ba."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Buhari shi kansa a baya sai da ya ajiye dan takaran yanzu saboda dukkansu Musulmai ne."

Babachir Lawal
Ba zamu yarda Tinubu ya dauki Musulmi matsayin abokin tafiyarsa ba, Babachir Lawal Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Babachir yace akwai bukatar jam'iyyar tayi nazari da kyau kafin zaben wanda zai yiwa Tinubu mataimaki.

"Rabuwar kai tsakanin addinai da kabilu ya karu. Kawai APC ta zabi Kirista mataimaki saboda mun san abinda PDP za tayi kenan."

2023: Tinubu zai lallasa Atiku a Adamawa, in ji Babachir Lawal

A wani labarin kuwa, Babachir Lawal, ya bayyana cewa Bola Tinubu zai kayar da Atiku Abubakar a jihar Adamawa a babban zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.

Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da Atiku, wanda zai daga tutar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sune manyan yan takara a zaben kasar mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kayi watsi da maganar addini ko kabila wajen zaben mataimakinka: Mataimakan gwamnoni ga Tinubu

Ana sanya ran Atiku wanda ya kasance dan asalin Adamawa ya kawo jihar a zabe mai zuwa amma tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya ce sam hakan ba mai yiwuwa bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng