Yanzu-Yanzu: Bayan shan kaye hannun Tinubu, Tsohon ministan Buhari ya lashe tikitin sanata a APC
- Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya lashe tikitin takarar sanata na jam'iyyar APC
- Akpabio, wanda ya janye wa Tinubu takara a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa, ya samu nasara ne a zaben da aka canza
- Tsohon ministan ya gode wa al'ummar mazaɓar Akwa Ibom ta arewa maso yamma bisa sake ba shi damar wakiltar su
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Akwa Ibom - Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya lashe tikitin takarar Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta arewa maso yamma a jam'iyyar All Progressive Congress wato APC.
Daily Trust ta ruwaito cewa Akpabio, wanda ya janye wa Bola Tinubu a zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa da aka kammala, ya samu nasara ne da kuri'u 478.
Kwamitin APC ya tantance Deleget 512 daga cikin guda 540, inda Sir Joseph Akpan ya samu kuri'a ɗaya, Ekpo Udom, wanda ya lashe zaben farko da aka shirya, ya samu kuri'u Uku, yayin da 11 suka lalace.
Da yake jawabi ranar Alhamis da daddare a Cibiyar tallafawa al'umma ta Godswill Akpabio da ke karamar hukumar Ikot Ekpene, wato wurin da aka canza zaben, tsohon ministan ya gode wa mutane bisa ganin cancantarsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Vanguard ta rahoto Akpabio ya ce:
"Ina gode wa mutanen mazaɓar Akwa Ibom ta arewa maso yamma bisa ganin na cancanta ku sake bani damar wakiltar ku a majalisar dattawan Najeriya. Na tuna lokacin da kuka bani irin wannan damar tsakanin 2015 zuwa 2019."
"Zan iya tuna cewa babu wani Sanata da ya tallafa muku kamar yadda na tallafa muku. Na san ayyukan da aka yi a sassan ƙananan hukumomi 10, tun daga na kasuwanni har da ayyukan ruwa, wuta, gini, da gina ɗakunan karatu."
Meyasa aka canza zaɓen?
Da yake jawabi tun farko, shugaban APC na jihar Akwa Ibom, Stephen Ntukekpo, ya ce uwar jam'iyya ta ƙasa ce ta umarci ya sake sabon zaɓe, ya kafa hujjar cewa an samu matsalolin rikici a na farko.
Ya ce:
"An samu matsaloli a zaɓen fidda ɗan takara na farko mako ɗaya da ya gabata kuma daga sama aka umarce ni da mu sake zabe. Muna da yan takara biyar kuma mun sanar da kowa."
A wani labarin kuma Karon farko bayan lashe zaɓen APC, Tinubu ya lallaɓa ya sa labule da shugaban ƙasa
Bayan lashe zaɓen fidda gwanin APC, tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, ya kai ziyara fadar shugaban ƙasa.
Tinubu tare da rakiyar gwamnan Legas da shugaban Oando Plc, sun gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng