Da Ɗumi-Ɗumi: Bola Tinubu ya sa labule da gwamnonin APC kan wanda zai zama mataimaki

Da Ɗumi-Ɗumi: Bola Tinubu ya sa labule da gwamnonin APC kan wanda zai zama mataimaki

  • Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da gwamnonin arewa na APC yanzu haka a Abuja kan wanda zai zama mataimakinsa
  • Rahoto ya nuna cewa aƙalla gwamnoni 10 ne suka halarci wurin taron tare da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu
  • Tinubu ya samu nasarar lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na APC ne bayan lashe zaben fidda gwani

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressive Congress wato APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yanzu haka ya shiga ganawa da gwamnonin arewa.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Tinubu na ganawa da gwamnonin arewa da suka hau madafun iko karkashin APC kan zabo wanda zai zama mataimakinsa a zaɓen 2023.

Haka nan daga cikin waɗan da suka halarci taron, har da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Kara karanta wannan

Tsohon dogarin Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa

Bola Tinubu tare da shugaban gwamnonin arewa, Simon Lalong.
Da Ɗumi-Ɗumi: Bola Tinubu ya sa labule da gwamnonin APC kan wanda zai zama mataimaki Hoto: The Plateau State Governor's Directorate of Press/facebook
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla gwamnoni 10 na arewa ne suka halarci taron wanda yanzu haka yake cigaba da gudana a Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda Tinubu ya samu nasarar lallasa sauran yan takara a babban taron APC na zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa.

Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ya sami kuri'u 1,271, kuma hakan ya ba shi damar lallasa yan takarar da ke binsa, tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Mambobin NWC sun ziyarci Tinubu

Mambobin kwamitin ayyuka (NWC) na jam'iyyar APC ta ƙasa sun ziyarci Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, ranar Alhamis.

Daily Trust ta ruwaito cewa mambobin NWC sun gana da Tinubu ne a gidansa da ke Abuja a karon farko tun bayan lashe tikitin takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Rigima bata ƙare ba: Bayan ganawa da Gwamnoni, BoT sun lallaɓa sun sa labule da Atiku kan mataimaki

Yayin ziyarar, shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, wanda ya jagoranci NWC zuwa gidan Tinubu, ya ce APC zata yi duk me yuwuwa ta tabbatar Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023.

Adamu ya ce mambobin NWC sum zama, "Sojojin kafa," na Bola Tinubu. inda a jawabinsa ya ce:

"Ka sha gagwarmaya kuma ka ga komai, ina mai tabbatar maka da cewa mun shirya fiye da faɗar fatar baki don ganin ka zama shugaban ƙasa."

A wani labarin kuma Tsohon dogarin Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya lashe zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa

Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya lashe zaben fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AA a zaɓen 2023.

Tsohon dogarin Marigayi Janar Sani Abacha, ya samu wannan nasara ne bayan lallasa abokin hamayyarsa da kuri'u 506.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262