Rigima bata ƙare ba: Bayan ganawa da gwamnoni, Atiku ya sa labule da PDP-BoT

Rigima bata ƙare ba: Bayan ganawa da gwamnoni, Atiku ya sa labule da PDP-BoT

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da mambobin kwamitim BoT sunyi wata ganawar sirri a Abuja ranar Laraba
  • Hasashe ya nuna cewa taron ba zai rasa alaƙa da zakulo wanda zai taimaka wa Atiku domin tunkarar babban zaɓen da ke tafe ba
  • Wata majiya ta kusa da BoT ta ce taron ya maida hankali ne kan zaben 2023, kalubalen da ƙasa ke ciki da haɗa kan PDP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP (BoT) sun gana da ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, a sirrance, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Mambobin BoT sun gana da tsohon mataimakin shugaban ƙasan ne ranar Laraba da yamma a Abuja ƙarƙashin jagorancin shugaban su, Sanata Walid Jibrin.

Atiku Abubakar.
Rigima bata ƙare ba: Bayan ganawa da gwamnoni, Atiku ya sa labule da PDP-BoT Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tun bayan kammala zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa a watan Mayu, BoT da Atiku Abubakar suka shirya zama domin tattauna wa kan wanda zai zama mataimaki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Atiku Abubakar ya aike da sakon murna ga Bola Tinubu bayan lashe tikitin APC

Wata majiya mai kusanci da BoT ta shaida wa wakilin jaridar cewa taron ya maida hankali kan abubuwan da suka shafi zaɓen 2023, ƙalubalen da Najeriya ke fama da su, da kuma uwa uba haɗin kan PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ana tsammanin taron ba zai rasa nasaba da zaɓen wanda zai zama mataimakin Atiku Abubakar ba a zaɓen 2023.

Su wa suka samu halartar taron?

Jiga-jigan mutanen da suka samu halartar taron sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Namadi Sambo, tsohon gwamnan Jigawa, Dakta Sule Lamido, da tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Emeka Ihedioha.

Sauran sune tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Maƙarfi, tsohon shugaban majalisar dattawa, David Marka, da sauran manya-manyan mutane.

Idan baku mance ba, ɗan takarar shugaban ƙasa wanda PDP ta tsayar, Atiku Abubakar, ya gana da gwamnonin da suka ɗare madafun iko karkashin inuwar PDP.

Kara karanta wannan

'Yan takarar shugaban kasa 7 da suka janye wa Bola Tinubu a filin taron APC

Har yanzun dai faɗi tashi bata kare ba tsakanin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP game da wanda ya dace su zaƙulo ya zama mataimakin Atiku domin tunkarar babban zaɓe.

A wani labarin kuma Atiku Abubakar ya aike da sakon murna ga Bola Tinubu bayan lashe tikitin APC

Ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya aike da sakon taya murna ga jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Atiku ya tura sako ne biyo bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na fitar da ɗan takara a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel