Tsohon dogarin Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa

Tsohon dogarin Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa

  • Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya lashe zaben fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AA a zaɓen 2023
  • Tsohon dogarin Marigayi Janar Sani Abacha, ya samu wannan nasara ne bayan lallasa abokin hamayyarsa da kuri'u 506
  • Al-Mustapha ya ce tsawon lokacin da ya shafe a aikin soja zai ba shi damar shawo kan matsalar tsaron Najeriya cikin sauki

Abuja - Tsohon babban jami'in tsaro na marigayi Janar Sani Abacha, lokacin da yake shugaban ƙasa a mulkin soja, Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya), ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Action Alliance (AA).

This Day ta ruwaito cewa tsohon dogarin tsohon shugaban ƙasan ya fafata a zaɓen fidda gwanin AA da wani ɗan takara, Samson Odupitan.

Tun kafin fara zaɓen yan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya guda biyu, Felix Osakwe da Tunde Kelani, suka janye, kuma suka ayyana goyon baya ga Al-Mustapha.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sawore ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa a AAC, zai gwabza da Atiku, Tinubu

Hamza Al-Mustapha.
Tsohon dogarin Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya lashe zaben fidsa ɗan takarar shugaban kasa Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Manjo Al-Mustapha mai ritaya ya samu kuri'u 506, inda ya yi nasarar lallasa abokin hamayyarsa Odupitan, wanda ya samu kuri'u 215.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin jawabi ga Deleget, shugaban jam'iyyar AA, Kenneth Udeza, ya ce an tantance masu ƙaɗa kuri'a 842 domin su zaɓi ɗan takara daga ckin mutum huɗu.

Jan hankalin da Al-Mustapha ya yi wa Deleget

Manjo Al-Mustapha ya faɗa wa Deleget cewa kwarewar da ya samu a matsayin jami'in soja na tsawon shekara 35 yayin aiki da Abacha zai bashi damar shawo kan matsalar tsaron ƙasar nan.

Leadership ta ruwaito Al-Mustapha ya ce:

"Ni mutum ne mai biyayya kuma ina da kwarewar da ake buƙata don fuskantar rashin tsaron ƙasar nan. Ni ɗan Najeriya ne da ya yi amanna da haɗin kanta, ina da kishin ƙasa duk da cin mutuncin da aka mun tsawon shekara 35 da na yi aiki."

Kara karanta wannan

Daga karshe, Shugaba Buhari ya magantu kan nasarar Bola Tinubu a zaɓen fidda gwanin APC

"Haɗin kan ƙasa ya fi ƙarfin a zauna teburin tattaunawa kuma jam'iyyar AA na da tsarin haɗa kan ƙasa, kasancewar jam'iyya ce ta kowa mai mambobi a lungu da saƙon ƙasar nan."

Mista Odupitan, bayan kammala zaɓen, ya ta ya Al-Mustapha murnan nasarar da ya samu tare da alƙawarin aiki tare da shi.

A wani labarin kuma rigima bata ƙare ba, bayan ganawa da gwamnoni, BoT sun lallaɓa sun sa labule da Atiku Abubakar a Abuja

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da mambobin kwamitim BoT sunyi wata ganawar sirri a Abuja ranar Laraba.

Hasashe ya nuna cewa taron ba zai rasa alaƙa da zakulo wanda zai taimaka wa Atiku domin tunkarar babban zaɓe n da ke tafe ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262