Da Dumi-Dumi: Sawore ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC

Da Dumi-Dumi: Sawore ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC

  • Omoyele Sawore ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a taron fidda gwani da ya gudana ranar Alhamis a Abuja
  • Sawore, mamallakin gidan jaridar Sahara Reporters ya samu nasarar ne ba tare da hamayya ba bayan aje muƙamin shugaban jam'iyya
  • Ya ce ya nuna wa duniya cewa yana da kwarewar da zai mulki Najeriya duba da zanga-zangar da ya jagoranta

Abuja - Mai gidan jaridar Sahara Reporters kuma jagoran tafiyar #TalkItBack, Omoyele Sowore, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar African Action Congress (AAC).

Vanguard ta ruwaito cewa mambobin AAC sun zaɓi Mista Sawore ba tare da hamayya ba a wurin babban taron zaɓen fidda gwani wanda ya gudana a ɗakin taron Work and Connect, Abuja.

Kara karanta wannan

Daga karshe, Shugaba Buhari ya magantu kan nasarar Bola Tinubu a zaɓen fidda gwanin APC

Omoyele Sawore.
Da Dumi-Dumi: Sawore ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC Hoto: Usoro Emmanuel/facebook
Asali: Facebook

Punch ta rahoto cewa Sawore ya yi murabus daga kan muƙaminsa na shugaban jam'iyyar AAC ranar Alhamis a wurin taron zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa.

Ya ce kwasutoshin ɗin jam'iyyar AAC ya haramta masa zama a kujerar shugaban jam'iyya yayin da yake neman tikitin takarar shugaban ƙasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan murabus daga shugaban jam'iyya, Sawore ya kuma gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, nan take Deleget suka amsa da, 'Aye' wato mun amince sai ka yi.

Zan iya shugabancin Najeriya - Sawore

Ya ce yana da duk abin da ake buƙata na jagorancin Najeriya kasancewar ya jagoranci zanga-zangar da ta jijjiga ƙasa da sauran abubuwan da suka auku a Najeriya.

A cewarsa ta hanyar zanga-zangar RevolutionNow da Endsars wanda ya yi iƙirarin farawa, ya samu damar taka wa gwamnati burki.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi na musamman gobe Lahadi

Sawore ya ce:

"Ba na son zama kamar sauran yan siyasa, saboda na yi murabus. Sauran jam'iyyu sun zaɓi ɓarayi a matsayin yan takararsu, na mu akwai banbanci."
"Mu matasa ne masu ilimin zamani, muna da zuciya da zummar canza abubuwa."

A ranar 2 ga watan Yuni, 2022, Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da Sawore a matsayin shugaban jam'iyyar AAC.

A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar SDP ta sanar da sakamakon zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa a 2023

Jam'iyyar S D P ta bi sahun sauran jam'iyyu yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen 2023 da ke tafe.

A ranar Laraba, SDP ta sanar da Adewole Adebayo, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa bayan ya lashe zaɓen fidda gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262