Adamu Aliero, Dakingari Da Wasu Jiga-Jigan APC a Kebbi Sama Da 30 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP
- Sanata Adamu Aliero da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin kasa sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Jihar Kebbi
- Aliero, cikin sanarwar da ya fitar da ya ce rashin adalci yayin zaben fidda gwani na gwamnoni da wasu matsalolin ne suka saka shi ficewa daga APC
- Tsohon ministan na Abuja ya ce ya tuntubi magoya bayansa da masu ruwa da tsaki kafin ya yanke shawarar komawa jam'iyyar ta PDP wacce ya ce za ta masa adalci
Jihar Kebbi - Tsohon gwamnan Jihar Kebbi Adamu Aliero da wasu jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress, APC a Jihar Kebbi sun fita daga APC sun koma PDP.
BBC Hausa ta rahoto cewa tsohon gwamnan ya ce rashin adalci da aka yi yayin zaben fidda gwani a Kebbi na daga cikin abubuwan da yasa suka fice daga APCn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aliero, wanda ya taba yin gwamna a Kebbi har sau biyu da kuma tsohon minista a Abuja ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar yana mai jadada rashin jin dadinsa kan yadda ake tafiyar da harkokin jam'iyyar ta APC a Kebbi.
Na tuntubi magoya baya na da masu ruwa da tsaki kafin in koma PDP, Aliero
Tsohon gwamnan ya ce sai da ya tuntubi magoya bayansa da masu ruwa da tsaki kafin ya dauki matakin komawa jam'iyyar ta PDP da za ta yi musu adalci wajen sake gina Najeriya.
Sanata Adamu ya koma PDP din ne tare da wasu jiga-jigan yan jam'iyyar APC fiye da 30, da suka hada da tsohon gwamnan Kebbi, Sa'idu Usman Nasamu Dakingari da Sanata Yahaya Abdullahi da tsohon mataimakin shugaban kwastam, Mohammad Mera.
Aliero ya yi kira ga magoya bayansa a Kebbi Central da wasu jihohin Najeriya su tabbatar sun zabi jam'iyyar APC a dukkan matakai, Daily Nigerian ta rahoto.
2023: Jam'iyyar ADC Ta Sanar Da Wanda Ya Lashe Zaben Fidda Gwaninta Na Shugaban Kasa
A wani rahoton, mai gidan talabijin din Roots Television, Dumebi Kachikwu, ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaben 2023, Premium Times ta rahoto.
Ya yi nasarar ne bayan kayar da yan takara irinsu Kingsley Moghalu, Chukwuka Monye, da wasy mutane takwas a yayin zaben fidda gwanin shugaban kasa da aka yi a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun a ranar Laraba.
Mr Kachikwu, kanin tsohon karamin ministan albarkatun man fetur, Ibe Kachikwu, ya yi nasarar ne bayan samun kuri'u 977 ya kada mai biye masa Mr Moghalu, Channels TV ta rahoto.
Asali: Legit.ng