Najeriya ta Dawo Hayyacinta, Za mu batar da Makasan Jama'a, Tinubu Ya Sha Alwashi
- 'Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Ahmed Asiwaju Bola Tinubu, ya sanar da cewa Najeriya ta dawo hayyacin ta
- A yayin da yake jawabin godiya bayan lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar mai mulki, Tinubu ya ce sai ya ga bayan kashe-kashen da ake yi a Najeriya
- Ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa zai yi duk abinda ya dace kuma iyakar karfinsa wurin kawo karshen rashin tsaro
Eagle Square, Abuja - 'Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola, ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa zai yi duk abinda ya dace kuma daidai karfinsa wurin dawo da kasar nan hayyacinta tare da magance matsalar kashe-kashe.
Tinubu yayin mika jawabin nasarar da ya samu, bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya ci zaben fidda gwani, ya ce kashe juna ba ya daga cikin cigaba, Vanguard ta ruwaito.
Ya ce, "Kauna tana nufin rungumar juna ne. Mu amince da cewa za mu gina kasa. Babu addinin da zai batar da wani a kasar."
Tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana kwarin guiwarsa kan cewa zai hada tawaga mai inganci kuma zai yi aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya samu kuri'u 1271 inda ya tabbata 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APc a zaben 2023 mai gabatowa.
Ya lallasa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya tashi da kuri'u 235 a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC da aka yi.
Zaben Fidda Gwani: Akwai Babban Hatsari da ke Kunno kai, NWC ga Tinubu da Sauran 'yan takarar Kudu
A wani labari na daban, Shugaban matasan jami'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya ja kunnen 'yan takarar shugaban kasa da shugabannin siyasar kudu a kan rashin hadin kai.
Kamar yadda ya ce, akwai 'yan takarar shugaban kasa na kudu suna tsaka mai wuya a zaben fidda gwanin jam'iyyar da ake yi.
Daga cikin 'yan takarar kudu sun hada da jagoran APC na kasa, Bola Tinubu, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi.
Asali: Legit.ng