Zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC: Jerin yan takara 4 da basu samu kuri’a ko daya ba

Zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC: Jerin yan takara 4 da basu samu kuri’a ko daya ba

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasar nan ta kammala zaben fidda gwaninta na shugaban kasa inda ta zabi dan takarar da zai daga tutarta a babban zaben mai zuwa a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tun farko dai an tantance yan takara 23 domin fafatawa a zaben bayan sun siya fom din takara na naira miliyan 100.

Zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC: Jerin yan takara 4 da basu samu kuri’a ko daya ba
Zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC: Jerin yan takara 4 da basu samu kuri’a ko daya ba Hoto: Punch/Premium Times
Asali: UGC

Sai dai kimanin yan takara 13 ne suka fafata a ranar zaben bayan wasu da dama sun sanar da janyewarsu daga tseren a filin babban taron.

Tsohon gwamnan jihar Lagas kuma babban jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaben da kuri'u 1, 271.

Sai dai kuma, akwai wasu yan takarar da aka fafata da su da basu samu kuri’a ko daya ba. Daga cikinsu harda tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Asiwaju Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng Hausa ta zakulo maku yan takarar da basu samu kuri’a ko daya ba kamar haka:

  1. Rochas Okorocha
  2. Tunde Bakare
  3. Tien Jack-Rich
  4. Ikeobasi Mokelu

Asiwaju Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC

A baya mun kawo cewa tsohon gwamna jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.

A zabensa na faako tun bayan barin muli a 2007, Tinubu yanzu shine zai wakilci jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa a zaben shekarar 2023.

Tinubu ya lallasa yan takarar da suka fafata a zaben inda ya samu kuri'u sama da 1,271 Wanda ya zo na biyu shine tsohon Gwamnan jihar Rivers, kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi wanda ya samu kuri'u 316.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: An fara kirgen kuri'u, Tinubu na gaba-gaba cikin 'yan takara

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng