Gwamna Bagudu ya bayyana dan takarar da za a kaddamar a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC
- Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi kuma shugaban gwamnonin APC, ya ce duk dan takarar da ya samu kuri'u mafi yawa shine za a ayyana a matsayin wanda ya lashe zabe
- Bagudu ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 7 ga watan Yuni, a Eagle Square filin babban taron jam'iyyar da ke gudana a yanzu haka
- Ya kuma bayyana cewa za a baiwa deliget uku daga kowace karamar hukuma damar kada kuri'a a zaben
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaban kwamitin babban taron APC kuma shugaban gwamnonin jam’iyyar, Atiku Bagudu, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa da ya samu kuri’u mafi yawa ne za a kaddamar a matsayin wanda ya lashe zabe.
Bagudu ya bayyana hakan ne a wajen babban taron jam’iyyar mai mulki na kasa da ke gudana a yau Talata, 7 ga watan Yuni, jaridar Thisday ta rahoto.
Ya ce yan tsirarun deliget da ke Eagle Square a daren yau sune za su sa tsarin ya zama mai sauki, sabanin lokacin da jam’iyyar ke da kimanin deliget 8,000 a babban taron na Maris.
A cewarsa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Deliget uku za a bari su kada kuri’a a kowace karamar hukuma bayan an tantance su. Za a kasance da wajen jefa kuri’a biyu. Za a kira jihohi biyu a lokaci guda.
“Deliget su rubuta sunan dan takarar da suke so da kyau, yayin da za a ba wadanda ba za su iya rubutu ba damar kiran wani deliget da suke so ya taimaka masu.
“Dan takarar da ya samu kuri’u mafi yawa ne za a kaddamar a matsayin wanda ya yi nasara. Duk dan takarar da ya yi muradin janyewa dole ya aikata haka a bainar jama’a sannan ya sanya hannu a fom din janyewa.”
Zaben fidda gwanin APC: Deliget din Jigawa ya yanki jiki, ya fadi matacce
A wani labarin, Punch ta ruwaito cewa, daya daga cikin wakilan jam'iyyar APC na Jigawa Alhaji Isah Baba Buji ya rasu yayin da yake wurin taron zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar a Abuja.
Ya fadi ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a safiyar ranar Talata a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa da ke Abuja.
Marigayin dai shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Jigawa ta tsakiya, inji rahoton jaridar The Nation.
Asali: Legit.ng