Da Duminsa: Jam'iyyar NNPP ta sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan Katsina

Da Duminsa: Jam'iyyar NNPP ta sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan Katsina

  • Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta gudanar da zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a zaɓen 2023
  • Injiniya Muhammad Nuru Khalil shi ne ya lashe tikitin NNPP bayan samun nasara kan abokin takararsa
  • Ɗayan ɗan takaran, Ibrahim Zakari, ya yi zargin aikata ba dai-dai ba yayin zaɓen, ya kuma sanar da janye wa

Katsina - Injiniya Nuru Khalil ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar Katsina na jam'iyyar NNPP Mai kayan maramari a zaben fidda gwani, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Khalil ya samu kuri'u 950 wanda ya ba shi damar lallasa babban abokin takararsa na kusa, Ibrahim Zakari Talba, wanda ya samu kuri'a 29.

Shugaban kwamitin zaɓen, Dakta Yusuf Ibarahim, ne ya sanar da sakamakon ranar Litinin bayan shafe sama da awanni biyu ana cuku-cukun zaɓe.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwani: 'Yan takarar Kudu maso Gabas sun tura wasika ga Buhari kan batun zabo magajinsa

Injiniya Muhammad Nuru Khalil.
Da Duminsa: Jam'iyyar NNPP ta sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Zaɓen ya ƙunshi Deleget 1, 154 daga sassan kananan hukumomi 34 da ke faɗin Katsina. Dakta Ibrahim ya ce daga cikin kuri'u 981 da aka kaɗa an samu guda biyu sun lalace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zaɓen fid da gwanin NNPP na ɗan takarar gwamnan ya gudana ne a sansanin baiwa matasa yan bautar ƙasa horo (NYSC) wanda ke kan hanyar Mani, cikin garin Katsina.

Haka nan kuma kwamitin zaɓe ya fara harkokin sauke nauyinsa ne da misalin ƙarfe 4:45 na yamma kuma ya ƙarƙare da ƙarfe 7:00 na dare.

Abubuwan da suka faru a wurin zaɓen

Kafin fara kaɗa kuri'a a wurin taron, sai da kwamitin NNPP ya ba kowane ɗan takara dama ya gaida Deleget bayan isowarsa wurin zaɓen fid da gwani.

Sai dai, Ibrahim Zakari, ya sanar da janye wa daga zaɓen bisa zargin rashin bin ƙa'idoji da dokoki da kuma haɗa baki da nufin shirya magudi.

Kara karanta wannan

'Yan Takarar Shugaban Kasa A APC Guda 7 Sun Ki Yarda Da Sunayen Mutum 5 Da Gwamnoni Suka Mika Wa Buhari

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta dare gida biyu bayan sanar da Lawan a matsayin ɗan takarar maslaha

Jam'iyyar APC fara tarwatse wa biyo bayan ayyana Sanata Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar shugaban kasa ta maslaha.

Sanata Abdullahi Adamu ya gaya wa sauran mambobin kwamitin NWC batun Lawan amma nan take suka yi fatali da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262