Abinda aka yiwa Abiola ake kokarin yiwa Tinubu, Ayo Fayose
- Ayo Fayose na jihar Ekiti ya yi kira ga Tinubu ya farga saboda tarihi na kokarin maimaita kansa
- Fayose yace irin martanin da wasu yan siyasa suka yiwa Tinubu kan ikirarin taimakawa Buhari abin lura ne
- Tsohon gwamnan Ekitin ya dade yana fadin cewa duk da ba jam'iyarsu daya da Tinubu ba, ba zai taba hada kai da masu yakarsa ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Legas - Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa wasu miyagu a fadar shugaban kasa na shirin yiwa Asiwaju Bola Tinubu irin abinda aka yiwa MKO Abiola.
MKO Abiola ne wanda ya lashe zaben shugaban kasan ranar 12 ga Yuni 1993 amma Babangida yayi watsi da sakamakon zaben.
Daga baya Gwamnatin Janar Sani Abacha ta garkameshi a kurkuku bayan alanta cewa shine shugaban kasa.
Bayan shekaru hudu ya mutu a gidan yari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Fayose ya bayyana hakan ne a budaddiyar wasikar da ya fitar ranar Litinin.
A wasikar, Fayose yace ya bayyana karara cewa ana shiryawa Tinubu tuggu kuma ya kamata ya farga da wuri.
A cewarsa:
"Dubi ga abubuwan da ke faruwa, ina ganin akwai wasu miyagu a jam'iyyarka da basu son ka. Hakazalika suna shirin yi maka abinda aka yiwa Awolowo da Abiola."
Fayose ya kara da cewa tuni an raba kan mabiyansa a dukkan jihohin kudu maso yamma shida.
Fayose, wanda dan PDP ne yace irin martanin da aka yiwa Tinubu kan jawaban da yayi a Abeokuta mako da ya gabata abin damuwa ne.
Asali: Legit.ng