Kano 2023: Sirikin Kwankwaso, Abba Gida-Gida ya tabbata 'dan takarar gwamna a NNPP

Kano 2023: Sirikin Kwankwaso, Abba Gida-Gida ya tabbata 'dan takarar gwamna a NNPP

  • Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya tabbata 'dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar NNPP
  • Deliget 1,452 na jam'iyyar daga gunduma 484 ne suka kada masa kuri'a duk da ya fito takarar babu abokin hamayya
  • Abba Gida-Gida ya mika sakon godiyarsa ga mambobin jam'iyyar, deliget da masu ruwa da tsaki kan yarje masa da suka yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Alhaji Abba Kabir-Yusuf ya samu tikitin takarar kujerar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar mai alamar kayan marmari ta NNPP.

Duk da Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya bayyana a takarar ba tare da abokin hamayya ba, ya tabbata 'dan takarar da kuri'u 1,452 na deliget a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Kano 2023: Sirikin Kwankwaso, Abba Gida-Gida ya tabbata 'dan takarar gwamna a NNPP
Kano 2023: Sirikin Kwankwaso, Abba Gida-Gida ya tabbata 'dan takarar gwamna a NNPP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Sanata Musa Bako ne ke kula da zaben fidda gwanin a hedkwatar jam'iyyar ta kasa.

Kara karanta wannan

Jajiberin Zaben Fidda Gwani: Buhari Ya Ci Abincin Dare Tare da Adamu da Gwamnoni

Bako ya yi bayanin cewa, tabbacin dole ne duk da Kabir Yusuf ne 'dan takarar gwamna daya tilo a jam'iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Deliget daga kowacce gunduma 484 na jihar sun tabbatar da shi a matsayin 'dan takarar kujerar gwamnan Kano a zaben 2023 da za a yi karkashin jam'iyyar NNPP," yace.

Jim kadan bayan tabbacin, Kabir Yusuf ya mika godiyarsa ga mambobin jam'iyyar, deliget da sauran masu ruwa da tsaki kan damar da suka bashi.

Ya yi kira ga mambobin da su dage tare da yin aiki tukuru wurin hadin kai domin nasarar jam'iyyar a zaben 2023.

Allah ne ya aiko Kwankwaso ya fatattaki yunwa, ya hada kan 'yan Najeriya, NNPP

A wani labari na daban, jam'iyyar NNPP ta kwatanta dan takarar shugabancin kasa a karkashin ta, Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin "ma'aikin Ubangiji" wanda yake son yakar yunwa da sake hada kan Najeriya.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya tono sirri: Ba dan ni ba da Buhari ya sha kaye a zaben 2015

Rahoton Daily Nigerian ya ce, Rabaren Emma Agubanze, mamban kwamitin tuntuba na addini na NNPP ya sanar da hakan a Legas a ranar Laraba. Ya ce za a yi zaben 2023 lafiya kalau kuma Kwankwaso ne da jam'iyyar za su yi nasara.

"Ya kasance a rubuce, ba Kwankwaso bane kadai batun. Gaskiyar lamarin, taimakon Ubangiji ya zo Najeriya a lokacin da zaben 2023 ke gabatowa.
"A don haka ne muke sanar da cewa, Sanata Kwankwaso ne Ubangiji ya aiko domin ya hada kan 'yan Najeriya kuma ya fara tun daga tushe," yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: