2023 ce Shekarar da Karyarku Za Ta Kare, Atiku Abubakar ga APC

2023 ce Shekarar da Karyarku Za Ta Kare, Atiku Abubakar ga APC

  • Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da yadda APC ta nuna halin ko in kula a kan harin da 'yan ta'adda suka kai Owo ta jihar Ondo
  • A cewar 'dan takarar, kadarin jam'iyya mai mulki na gab da karyewa a zaben shugaban kasar da za a yi a shekarar 2023
  • Ya kara da cewa duk da yadda jinin salahan bayi ke kwarara a titi da tsakar rana bai hana jam'iyyar gabatar da zaben fidda gwaninta ba a cikin kwanakin aiki

'Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce wa jam'iyya mai mulki dubunta zai cika a zaben 2023.

Atiku ya ce jam'iyya mai mulki ta APC ta gaza bayyana damuwarta game da wadanda 'yan ta'adda suka kai wa farmaki a Owo, jihar Ondo yayin da gaba daya kasar ke cikin jimami.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan hanyar da za a bi wajen zabar dan takarar APC

Sannan ta gaza fasa gabatar da taro da 'yan takarar shugaban kasarta a ranar da aka kai harin, inda ya siffanta hakan da halin ko in kula.

A wata takarda da hadimin 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar PDP, Paul Ibe, ya bayyana hakan a ranar Litinin, Punch ta ruwaito.

A cewar Atiku, ba dalili bane a ce don ana gabatar da zaben fidda gwanin jam'iyyar duk da rahoton da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya samu amma duk da haka ya samu kwarin guiwar zaben wanda zai gajeshi.

"Yana da mahimmaci a san cewa zaben shugaban kasar shekarar 2023, fiye da komai alama ne da ke nuna yadda APC ta gaza, saboda haka kada 'yan Najeriya su damu da gazawarsu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk da yadda jinin salahan bayi ke kwarara a titin jihar a tsakar rana, hakan bai hana shugabannin jam'iyyar APC taruwa a Abuja tare da gabatar da taron a cikin wani yanayi da ke bayyana rashin tausayin kasa," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Majiyar Cikin Gida Ta Fallasa Sunan 'Dan Takarar da Buhari ya Karkata Hankali Wurinsa

"Har ila yau, abun takaicin da APC ta kira da zaben fidda gwani wanda kawai nada 'dan takara aka yi, yana da kyau a tambaye shugabannin jam'iyyar dalilin da yasa suka zabi gabatar da abun da suke kira da zaben fidda gwani a cikin ranakun aiki, wanda hakan ya dagula lamurran tattalin arzirki a cikin birnin tarayyar.
"Ko da wakilan zabe a abun da suka kira da zabe suka shiga babban birnin tarayyar, sun fuskanci dogon layin siyan man fetur da duhun da ya cigaba da dawainiya da babban birnin saboda rashin wutar lantarki," Yace.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce mazauna birnin tarayyar wadanda suka dade suna fuskantar tsananin rayuwar yau da kullum sanadiyyar shugabanci mara kyau na jam'iyya mai mulki, zabar mahimman ranakun aiki - Litinin da Talata - saboda zaben fidda gwanin APC alama ne na son zuciya.

"Ba sai an ambaci koma waye aka dauka a matsayin 'dan takarar shugaban kasar APC a cikin irin wannan yanayin ba zai canza zare daga irin mulkin kama karyan da APC ke yi ba.

Kara karanta wannan

Shugabancin kasa a 2023: Ni ne muryar matasa da mata, Gwamna Yahaya Bello

"Irin wannan 'dan takarar ba zai wakilci 'yan Najeriya da cika musu buri bayan halin da jam'iyya mai mulkin aka san ta da shi ba," a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng