Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa a APC ya janye saboda wasu dalilai

Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa a APC ya janye saboda wasu dalilai

  • Sanata Ken Nnamani ya fasa tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben fidda gwani da za a yi a ranar Talata 7 ga watan Yuni
  • Tsohon shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 6 ga watan Yuni a babban birnin tarayya Abuja
  • Janyewar Nnamani daga takarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan sanar da Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ken Nnamani, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya fice daga takarar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, TheCable ta ruwaito.

Tsohon dan majalisar ya bayyana janyewarsa ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Fitaccen dan takarar APC ya janye daga takara
Da dumi-dumi: Dan takarar shugaban kasa a APC ya janye saboda wasu dalilai | Hoto: Senator Ken Nnamani, GCON
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito shi yana cewa:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan hanyar da za a bi wajen zabar dan takarar APC

“A halin da ake ciki yanzu, ba wani ma’ana in ci gaba da takara domin ban samu damar tallata bayanai na da ra’ayoyina ga wakilan jam’iyyarmu ba ta hanyar da za ta ba da damar shawarwari da fahimtar juna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Saboda haka, na hadiye buri na, ina yi wa jam’iyyar fatan samun nasara a zaben fidda gwani da kuma hadin kai domin mu samu nasarar lashe zaben 2023.
“Zan ci gaba da cudanya da jam’iyyar da shugabanninta domin ganin cewa tunani da dabi’un da nake so da yadawa sun samu gindin zama a cikin harkokin mulkin jam’iyyar da kuma shugabancin jama’a bayan zabe.”

Ba za a kakabawa APC dan takarar shugaban kasa ba, inji Buhari

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba za a kakaba dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa ba, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta dare gida biyu bayan sanar da Lawan a matsayin ɗan takarar maslaha

A cewar wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa Buhari ya fitar, Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani taro da gwamnonin APC na yankin Arewa suka yi.

Kalaman shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya amince da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.