Da Ɗuminsa: Jam'iyyar APC ta karyata zaban Lawan a matsayin ɗan takarar Maslaha

Da Ɗuminsa: Jam'iyyar APC ta karyata zaban Lawan a matsayin ɗan takarar Maslaha

  • Kwamitin NWC na jam'iyyar APC ta ƙasa ya musanta tsayar da Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar maslaha a zaɓen 2023
  • Sakataren tsare-tsare, Sulaiman Argungu, ya ce ba zasu kaucewa abin da gwamnonin arewa da kudu suka yanke ba
  • A gobe Talata, APC ta tsara gudanar da zaben fidda gwaninta na kuherar shugaban kasa

Abuja - Kwamitin gudanarwa na APC ta ƙasa (NWC) ya ce bai zaɓi Sanata Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar masalaha na APC a zabem 2023 ba, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Wasu rahotanni da suka karaɗe kafafen watsa labarai ranar Litinin sun nuna cewa Shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu da mambobin NWC sun amince da Lawan ya karɓi tutar APC.

Tutar jam'iyyar APC.
Da Ɗuminsa: Jam'iyyar APC ta karyata zaban Lawan a matsayin ɗan takarar Maslaha Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Amma da yake jawabi a wurin taron manema labara a Hedkwatar APC ta ƙasa, Sakataren tsare-tsare, Sulaiman Argungu, yaxe rahotannin duk ƙanzon kurege ne kuma mara amfani.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan hanyar da za a bi wajen zabar dan takarar APC

Argungu ya bayyana cewa gwamnonin kudu da arewa sun amince da miƙa mulki hannun yan kudu, inda ya kara da cewa kwamitin NWC ba zai yi wani abu da ya saɓa wa haka ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ra'ayin Adamu ne kaɗai na zaɓan Lawan - mambobin NWC

Argungu ya tabbatar da cewa Adamu ya sanar da su zaɓen Lawan a matsayin ɗan takarar Masalaha, sanarwa kaɗai, ba wani abu bane da ya kawo a tattauna.

The Cable ta ruwaito Sakataren ya ce:

"Shugaban APC, Abdullahi Adamu, ya yi mana cikakken bayani na zaɓan Lawan a matsayin ɗan takarar masalaha, bayani kawai ya mana, ba wani abu bane da aka tattauna."
"Kuna da masaniyar cewa gwamnonin arewa sun amice a kai takara kudu, takwarorin su na kudu na bayan su, saboda haka mu mambobin NWC muna tare da gwamnoni."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta dare gida biyu bayan sanar da Lawan a matsayin ɗan takarar maslaha

Bayanai sun nuna cewa jam'iyyar APC na ta faɗi tashi da kokarin tsayar da ɗan takararta na shugaban ƙasa ta hanyar masalaha a zaɓen 2023.

Babban taron jam'iyya mai mulki na musamman wanda Deleget 2, 340 zasu zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa zai gudana ne gobe Talata.

A wani labarin kuma Ban janye wa kowa takara ba, Gwamnan APC da ke mafarkin gaje Buhari ya magantu

Gwamna Fayemi na Ekiti ya musanta raɗe-raɗin da ke cewa ya janye wa mataimakin shugaban kasa takara a APC.

A wata sanarwa da ya fitar ta hannun daraktan Kamfen dinsa, gwamnan ya ce yana da goyon bayan masu ruwa da tsaki a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262