Yanzu-Yanzu: Ba za a kakabawa APC dan takarar shugaban kasa ba, inji Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ba za a kakabawa 'yan APC dan takarar da bai kwanta musu ba
- Shugaban ya bayyana hakan ne bayan ganawa da gwamnonin APC na yankin Arewacin kasar nan a Abuja
- Shugaba Buhari ya gana da su ne don tattauna batun da ke alaka da zaben fidda gwanin jam'iyyar APC da za a yi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba za a kakaba dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa ba, TheCable ta ruwaito.
A cewar wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa Buhari ya fitar, Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani taro da gwamnonin APC na yankin Arewa suka yi.
Kalaman shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya amince da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar.
A cewar sanarwar da muka gani a jaridar Daily Trust:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“An zabe ka kamar yadda aka zabe ni. Ka zama mai hankali kamar yadda nake. Allah ya bamu dama; ba mu da dalilin korafi. Dole ne mu kasance a shirye don daukar zafi kamar yadda muke daukar farin ciki. A bar wakilai su yanke shawara. Dole ne jam’iyyar ta shiga, babu wanda zai nada kowa.”
Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa a APC ya janye saboda wasu dalilai
A wani labarin, Ken Nnamani, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya fice daga takarar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, TheCable ta ruwaito.
Tsohon dan majalisar ya bayyana janyewarsa ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja ranar Litinin.
A cewarsa:
“A halin da ake ciki yanzu, ba wani ma’ana in ci gaba da takara domin ban samu damar tallata bayanai na da ra’ayoyina ga wakilan jam’iyyarmu ba ta hanyar da za ta ba da damar shawarwari da fahimtar juna.
Asali: Legit.ng