Yanzun Nan: Fadar shugaban ƙasa ta maida wa Tinubu martani kan taimaka wa Buhari a 2015

Yanzun Nan: Fadar shugaban ƙasa ta maida wa Tinubu martani kan taimaka wa Buhari a 2015

  • Fadar Shugaban kasa ta ce babu wani mutum ɗaya da zai bugi kirjin shi yace shi ya kai Buhari ga nasara a shekaru Bakwai da suka wuce
  • Yayin raddi kan ikirarin Bola Tinubu a wata sanarwa, fadar shugaban ta ce miliyoyin yan Najeriya ne suka kaɗa wa Buhari kuri'un su
  • Ta ce tabbas wasu tsirarun mutane ne suka haɗa APC, dubbanni suka aiwatar yayin da miliyoyi suka yi zaɓe

Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Miliyoyin yan Najeriya ne suka zaɓi Buhari ya shiga ofishin shugaban ƙasa a shekarar 2015.

Babu wani mutum ɗaya da zai yi ikirarin cewa shi ya taimaka wa Buhari ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2015, a cewar fadar ta shugaban ƙasa, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta dare gida biyu bayan sanar da Lawan a matsayin ɗan takarar maslaha

Fadar shugaban ƙasa ta yi wannan kalaman ne yayin martani ga ikirarin jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Yanzun Nan: Fadar shugaban ƙasa ta maida wa Tinubu martani kan taimaka wa Buhari a 2015 Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, fadar ta ce abun da yawuce ba shi da alaƙa da zaɓe na gaba, abinda ya dace shi ne ta ya za'a zakulo shugaba, "Wanda zai ɗaga Najeriya fiye da yadda take."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fadar shugaban ƙasa ta ce:

"Ba wani abun mamaki bane a lokacin da zaɓen fidda gwanin APC ke gabatowa wani ɗan takara ya alaƙanta kansa da nasarar shugaban kasa shekara 7 da ta wuce."
"Mutane da yawa sun ba da gudummuwa, karami da babba, har ya kafa tarihi a matsayin ɗan takarar adawa na farko da ya kayar da shugaban kasa mai ci cikin kwanciyar hankali a akwatin zaɓe."

Kara karanta wannan

Zabo dan takara: Buhari ya shiga ganawar sirri da gwamnonin APC na Arewa

"Mutane sun shawarci shugaban ƙasa ya nemi takara, waɗanda su suka yanke haɗa sabuwar jam'iyya (APC) wacce ta zama sanadin lallasa dukkan sauran jam'iyyu kuma ta samu nasara."

Yadda Buhari ya samu nasara a 2015

A ruwayar Punch, fadar shugaban ƙasan ta ƙara da cewa:

"Wasu mutane yan kalilan ne suka yanke hukuncin, dubbanin suka aiwatar yayin da miliyoyi suka kaɗa kuri'u. Babu wani mutum ɗaya da zai ikirarin shi kaɗai ya sa abun ya yuwu.

A wani labarin kuma Abin da 'yan takara suka faɗa wa Buhari game da wanda zai zaɓa ya gaje shi a 2023

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce a wurin ganawarsu da shugaba Buhari sun amince su koma bayan duk wanda ya zaɓa.

Gwamnan ya ce jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu na wurin taron kuma bai musa kan matsayar ba, don haka ya amince.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262