2023: Malam Shekarau da sauran yan takara biyu da suka lashe tikitin Sanata a zaɓen fidda gwanin NNPP a Kano

2023: Malam Shekarau da sauran yan takara biyu da suka lashe tikitin Sanata a zaɓen fidda gwanin NNPP a Kano

  • Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya samu nasara a zaɓen fitar da yan takarar Sanata na jam'iyyar NNPP
  • Shekarau wanda ya fice daga jam'iyyar APC kwanakin baya, ya lashe tikitin ne ba tare da hamayya a Gezawa, Hedkwatar ƙaramar hukumar Gezawa a Kano
  • Jam'iyya mai tashe wato NNPP mai kayan marmari ta sanar da sauran yan takararta na sanatan Kano ta kudu da arewa

Kano - Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya lashe tikitin takarar Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, (NNPP).

Daily Nigerian ta rahoto cewa Malam Shekarau ya lashe zaɓen ne ba tare da abokin hamayya ba domin neman tazarce kan kujerar da yake kai a yanzu.

Yan takarar Sanata a NNPP.
2023: Malam Shekarau da sauran yan takara biyu da suka lashe tikitin Sanata a zaɓen fidda gwanin NNPP a Kano Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta gudanar da zaɓen fitar da yan takarar ne a garin Gezawa, Hedkwatar ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

Malam Shekarau, tsohon gwamnan Kano na tsawon zango biyu kuma Sanata mai ci, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar APC zuwa NNPP bayan saɓanin da ya shiga tsakaninsa da Ganduje.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu bayanai sun nuna cewa ya ɗauki matakin ficewa daga APC ne bayan gaza samun tikitin cigaba da wakiltar al'ummar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa.

Sauran mutum biyu da suka lashe tikitin Sanata a Kano

Haka nan kuma, Dakta Abdullahi Baffah, shi ne aka bayyana a matsayin wanda ya lashe tikitin NNPP na kujerar Sanata mai wakiltar Kano ta arewa, kamar yadda The nation ta ruwaito.

Sai kuma tsohon hadimin shugaban ƙasa kan harkokin majalisar wakilai ta ƙasa, Honorabul Kawu Sumaila, wanda ya ci nasarar samun tikitin sanatan Kano ta kudu karkashin NNPP.

Hakan na nufin waɗan nan yan takara uku ne zasu fafata a babban zaɓen 2023 da ke tafe karkashin NNPP mai tashe musamman a jihar Kano.

Kara karanta wannan

APC ta gamu da babban cikas, Ɗan takarar gwamna da dubbannin magoya baya sun fice daga jam'iyyar

A wani labarin kuma gwamna Yahaya Bello ya faɗi Abin da yan takara suka faɗa wa Buhari game da wanda zai zaɓa ya gaje shi a 2023

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce a wurin ganawarsu da shugaba Buhari sun amince su koma bayan duk wanda ya zaɓa.

Gwamanan ya ce jagoran APC na ƙasa , Bola Tinubu na wurin taron kuma bai musa kan matsayar ba, don haka ya amince.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262