2023: Kowa ya cije kan bakansa, an gaza yin sulhu da Tinubu da su Osinbajo a takaran APC

2023: Kowa ya cije kan bakansa, an gaza yin sulhu da Tinubu da su Osinbajo a takaran APC

  • Jagororin siyasar Kudu maso yammacin Najeriya su na kokarin sasanta kan masu takara a APC
  • Amma wannan yunkuri bai haifar da ‘da mai ido ba, masu neman tikitin ba su da niyyar hakura
  • Akwai ‘yan siyasa akalla bakwai daga yankin kudu maso yamma da ke harin shugaban kasa a APC

Lagos - Yunkurin dattawan Kudu maso yamma na samar da ‘dan takarar shugaban kasan 2023 ta hanyar maslaha ya ci tura a jam’iyyar APC mai mulki.

Daily Trust ta fitar da rahoto da ya bayyana cewa maganar sasanta mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da irinsu jigon APC, Bola Tinubu ya gagara.

A ranar Lahadin da ta gabata, manyan ‘yan siyasan kudu maso yammacin Najeriya suka cigaba da bakin kokarinsu na ganin sun samu hadin-kai a APC.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Majiyar Cikin Gida Ta Fallasa Sunan 'Dan Takarar da Buhari ya Karkata Hankali Wurinsa

Jagororin da ke kokarin hada-kan masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a yankin sun hada da Cif Bisi Akande da kuma Olusegun Osoba.

Babu mamaki Olusegun Osoba ya yi zama da Bola Tinubu da Farfesa Yemi Osinbajo, Kayode Fayemi, da su Ibikunle Amosun a gidansa da ke Legas.

Zabe ya karaso, kai bai hadu ba

Amma a karshen zama da aka yi, ba a iya cin ma matsaya a kan wanda za a tsaida takara ba. Maganar da ake yi nan da gobe za ayi zaben tsaida gwani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawan, Buhari da Osinbajo
Jagororin APC a taro Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Wadanda suka samu labarin abin da ya faru wajen taron sun shaida cewa Farfesa Osinbajo da Bola Tinubu duk sun nuna ba su da niyyar janye takara.

Su wanene masu neman tikiti a APC

‘Yan siyasar Kudu maso yamma da suke neman APC ta tsaida su a 2023, sun hada da Yemi Osinbajo, Bola Tinubu, Hon. Dimeji Bankole, da Kayode Fayemi.

Kara karanta wannan

Matakai 3 da Tinubu zai iya dauka idan bai samu tikitin shugaban kasa na APC ba

Sannan a cikin masu son takara akwai, Ibikunle Amosun, Robert Ajayi Boroffice da Fasto Tunde Bakare.

Majiyar take cewa ana tunanin Asiwaju (Tinubu) da mataimakin shugaban kasa za su gwabza ne, domin an gagara shawo kan daya wani daga cikinsu ya janye.

Darektan yada labarai da sadarwa na kwamitin yakin Tinubu Campaign Organisation, Mista Bayo Onanuga ya ce su na jiran a gwabza a zaben fitar da gwani.

Jaridar ta ce Bayo Onanuga ya nuna babu maganar janye takara, abin da ya rage kurum shi ne a shiga zaben tsaida gwani domin a ga wanda zai samu takara.

A kai takara Kudu - Gwamnonin APC

A baya kun samu rahoto, Gwamnonin Arewa sun rubutawa Mai girma Muhammadu Buhari takarda cewa Gwamnan Jigawa ya hakura da neman takara.

Hakan na zuwa ne a bayanin matsayar da Gwamnonin Arewan na APC suka dauka game da zaben 2023, suka bada shawarar a mikawa 'dan kudu takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng