Zaben fidda gwanin APC: Jerin sunayen titunan da aka karkatar da zirga-zirgar ababen hawa a Abuja

Zaben fidda gwanin APC: Jerin sunayen titunan da aka karkatar da zirga-zirgar ababen hawa a Abuja

  • Kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya ta Abuja, Adeh Josephine, ta sanr da karkatar da zirga-zirgar ababen daga wasu manyan tituna
  • Kamar yadda Adeh ta sanar, an yi hakan ne domin zaben fitar da gwani na 'dan takarar shugabancin kasa na APc da za a yi a Eagle Square
  • Ta ce a titunan da suka hada da titin Goodluck Ebele Jonathan, titin kotun daukaka, ECOWAS da sauran wuraren duk za a dinga caje ababen hawa

FCT, Abuja - Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya na Abuja, sun sanar da karkatar da zirga-zirgar ababen hawa kafin zaben fitar da gwani na takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC wanda za a yi a ranakun 6 da 7 na watan Yuni a Abuja.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Josephine Adeh, ta sanar da hakan ne a wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Yan Sanda Sun Bayyana Sunan Mutumin Da Aka Kashe Kuma Aka Kona Shi a Abuja Saboda Batanci, An Fara Bincike

Zaben fidda gwanin APC: Jerin sunayen titunan da aka karkatar da zirga-zirgar ababen hawa a Abuja
Zaben fidda gwanin APC: Jerin sunayen titunan da aka karkatar da zirga-zirgar ababen hawa a Abuja. Hoto daga dailytust.com
Asali: UGC

Ta ce rundunar ta sanya tsarin tsaro domin bai wa babban birnin tarayyan tsaro a lokacin da gaba.

Adeh ta ce, karkartarwar da sauran tsarin tsaro da aka kara kan wadanda akwai an yi shi ne saboda yawan bakin da ke shigo babban birnin tarayyan ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce za a karkartar da zirga-zirgar ababen hawa a titin Goodluck Ebele Jonathan, titin kotun daukaka kara da ECOWAS kusa da ma'aikatar harkokin mata da ta kudi.

Adeh ta ce, za a karkartar da zirga-zirgar ababen hawa kusa da ma'aikatar harkokin wake, Kur Mohammed kusa da Masallacin kasa, Benue Plaza, Nitel Junction, NNPC Tower da gadar Ceddi Plaza.

Ta ce sauran wuraren da aka karkartar da zirga-zirgar ababen hawa su ne Gana kusa da Transcorp, Hedkwatar DSS, NASS Junction, Bullet da Bayelsa House.

Adeh ta ce za a tura jami'ai masu yawa da za su taimaka wurin gyara tsarin zirga-zirgar ababen hawa domin taimakawa masu ababen hawa. Za kuma a dinga tsayar da ababen hawa tare da masu yawo a kafa ana duba su tare da abinda suke dauke da shi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Mun daina adana muhimman kayayyakin zabe a CBN, INEC

2023: INEC ta saki jerin ka'idojin zabuka, ta sanar da irin takardun kuri'u da za a kirga

A wani labari na daban, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta fitar da jerin ka'idojin da za a yi amfani da su wurin aiwatar da zaben 2023 na kasa da ke karatowa.

Kamar yadda ka'idojin su ka zo, wajibi ne shugaban akwatin zabe, PO, ya kirga yawan takardun zabe wadanda suke dauke da hatimin hukumar, jaridar Leadership ta ruwaito.

A batun amfani da wayoyi yayin zabe, kamar yadda dokokin su ka nuna, wajibi ne kawar da duk wata waya ko na'urar da za a iya amfani da ita wurin daukar hotuna a harabar zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng