Da duminsa: Mun daina adana muhimman kayayyakin zabe a CBN, INEC

Da duminsa: Mun daina adana muhimman kayayyakin zabe a CBN, INEC

  • Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ya ce sun daina adana muhimman kayayyakin zabe a CBN
  • Mahmud Yakubu ya sanar da cewa ba su taba samun wata matsala da Babban Bankin Najeriyan ba tunda suka fara wannan hadakar da su ba
  • Ya kara da bayyana cewa, za su samar da wata mafita da wurwuri tun kafin zaben gwamnonin jihar Ekiti wanda a za a yi a ranar 16 ga Yuni

FCT, Abuja - Mahmood Yakubu, shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ya ce muhimman kayayyakin zabe na hukumar an daina kai su babban bankin Najeriya, CBN.

Shugaban INEC din ya ce hukumar zabe ba ta taba samu wata matsala da babban bankin ba tun bayan fara wannan hadakar, amma saboda "halin da ake ciki yanzu", za a samo wata mafitar.

Kara karanta wannan

2023: INEC ta saki jerin ka'idojin zabuka, ta sanar da irin takardun kuri'u da za a kirga

Da duminsa: Mun daina adana muhimman kayayyakin zabe a CBN, INEC
Da duminsa: Mun daina adana muhimman kayayyakin zabe a CBN, INEC. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yadda za a dauka sabbin matakai da wuri tun daga zaben gwamnan jihar Ekiti na ranar 16 ga watan Yuni a jihar Ekiti.

Yakubu ya sanar da hakan ne a ranar asabar yayin da ake tattaunawa da shi kan "Masu kada Kuri'u" wanda "Ya isa Haka" suka shirya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2023: INEC ta saki jerin ka'idojin zabuka, ta sanar da irin takardun kuri'u da za a kirga

A wani labari na daban, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta fitar da jerin ka'idojin da za a yi amfani da su wurin aiwatar da zaben 2023 na kasa da ke karatowa.

Kamar yadda ka'idojin su ka zo, wajibi ne shugaban akwatin zabe, PO, ya kirga yawan takardun zabe wadanda suke dauke da hatimin hukumar, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ni a suwa: Ba zan taba kuskura na raina shugaba Buhari ba, inji Bola Tinubu

A batun amfani da wayoyi yayin zabe, kamar yadda dokokin su ka nuna, wajibi ne kawar da duk wata waya ko na'urar da za a iya amfani da ita wurin daukar hotuna a harabar zabe.

Sannan dokar ta tabbatar da cewa ba za ayi amfani da sakamakon wani akwati ba wanda yawan kuri'u ya zarce yawan masu zaben da aka tantance, kuma wajibi ne jami'in da ke da alhakin tattara kuri'u ya bayar da rahoto idan hakan ya auku.

Haka zalika tazarar da ke tsakanin 'yan takara biyu wadanda su ka fi yawan kuri'u kamar yadda dokar ta tanadar, ba yawan masu zaben da su ka amshi katinan zabensu ba ne (PVCs) a wurin zaben da aka dage zabe, ko aka rushe shi ko kuma ba a gudanar da shi ba kamar yadda sashi na 24(2 & 3), 47(3) da 51(2) na dokar zaben 2022 ya tanadar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dandazon jama'a tarbi Tambuwal a Sokoto bayan zaben fidda gwanin PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng