Shirin 2023: APC ta magantu kan batun takarar Jonathan a zaben fidda gwanin shugaban kasa
- Kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa a APC ya mika rahoto, ya ce tsohon shugaba Jonathan ba ya APC
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyar ta sanar da ware 'yan takara 13 da za su fafata a zaben fidda gwanin jam'iyyar
- A baya an sha yada jita-jita cewa Jonathan zai sake tsayawa takara a karkashin jam'iyyar APC mai mulki a 2023
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa a APC a ranar Juma’a ya musanta batun tantance tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan cikin 'yan takara.
Shugaban kwamitin tantancewar, John Odigie-Oyegun, ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a lokacin da ya mika rahotonsa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abduallahi Adamu, a wani taron kwamitin ayyukan jam'iyyar na kasa.
Odigie-Oyegun ya shaidawa manema labarai cewa sabanin labaran da ake yadawa, tsohon shugaban bai halarci taron tantancewan da aka yi Transcorp Hilton ba, inji rahoton Punch.
Bayanin Oyegun ya biyo bayan rahotannin da ke cewa jam’iyyar ta rage sunayen ‘yan takarar shugaban kasa daga 23 zuwa 13.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayanin da jigon na APC ya yi ya kara tabbatar da rahoton jaridar Guardian da ke cewa tsohon shugaban kasar bai halarci taron tantance 'yan takara da APC ta gudanar a kwanakin nan ba.
ASUU: Gwamnatin Buhari ta yi kwana da kudaden 'yan Najeriya, za su kashe a zabe
A wani labarin, kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta zargi jiga-jigan siyasar Najeriya da kwashe kudaden Najeriya gabanin babban zaben 2023 maimakon magance matsalolin da ke addabar ilimi a kasar.
Shugaban kungiyar ASUU, reshen jami’ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole ne ya bayyana hakan, inda ya kara da cewa gwamnati ta koma tattaunawa da kungiyar duk da cewa sabanin yarjajeniyar farko ne, rahoton Leadership.
A cewarsa, gwamnati da ASUU za su duba daftarin yarjejeniyar 2009 ta ASUU/FGN wacce tawagar gwamnati ta fara tare da ASUU a 2007 kuma aka kammala shi a watan Mayu, 2021.
Asali: Legit.ng