2023: Kwamitin tantancewar APC ya kori 10 daga cikin 'yan takarar shugaban kasa

2023: Kwamitin tantancewar APC ya kori 10 daga cikin 'yan takarar shugaban kasa

  • Kwamitin tantance 'yan takara a APC ya yi tankade da rairaya, ya kori 10 daga cikin 'yan takarar da suka sayi fom din APC
  • Kwamitin ya ce matasa masu jini a jika aka zaba domin su fafata a zaben fidda gwanin da za a gudanar
  • Sai dai, har yanzu ba a samu sunayen mutanen da aka dakatar din ba, duk da cewa a makon gobe ne za a yi zaben

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Wani rahoton da This Day ta fitar ya ce, kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya kori mutane 10 da za su fafata a zaben fidda gwani da za a yi a mako mai zuwa.

Shugaban kwamitin, John Oyegun ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Takarar Tinubu, Osinbajo, Amaechi da Lawan a 2023 ta na raba kawunan na-kusa da Buhari

A cewar Mista Oyegun, 13 ne kawai cikin 23 da kwamitin ya tantance za su fafata a zaben na mako mai zuwa.

An haramtawa tsofaffi shiga zaben fidda gwanin APC
Yanzun nan: Kwamitin tantancewar APC ya kori 10 daga cikin 'yan takarar shugaban kasa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya kara da cewa matasa ne kawai suka shiga jerin sunayen wadanda aka wanke su yi takara a jam'iyyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai da aka tambaye shi ko su wanene wadanda aka hana su takara, Mista Oyegun ya ki bayyana sunayensu.

Kwamitin ya gudanar da aikin tantancewar ne tsakanin Litinin zuwa Talatar wannan makon.

Ana sa ran ’yan takarar da aka tantance za su fafata a zaben fidda gwani na shugaban kasa a Abuja tsakanin ranakun 6 zuwa 8 ga watan Yuni.

Batutuwa na ci gaba da fitowa kan shirin da jam'iyyar mai ci ke yi nan da zabenta na fidda gwani da ke tafe nan kusa.

Tinubu: Buhari dan Arewa ya dana mulki shekara 8, 2023 ta mu ce, mu Yarbawa

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, a ranar Alhamis, ya bayyana cewa yanzu lokaci ne da Yarabawa za su kawo shugaban Najeriya na gaba a 2023.

Tinubu ya bayyana haka ne a dakin taro na masaukin shugaban kasa dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga deliget-deliget din APC gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Tinubu, wanda ya ce lokacin Yarbawa ne yanzu, ya kuma lura cewa lokaci ya yi da zai zama shugaban kasa, inji rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.