Jam'iyyar APC ta gamu da babban cikas, Ɗan takarar gwamna da dubbannin magoya baya sun fice daga jam'iyyar
- Yayin da APC ke shirin zaben fidda ɗan takararta na shugaban ƙasa, jam'iyyar ta yi babban rashi na mambobinta a jihar Oyo
- Ɗan takarar gwamna da ya sha ƙasa, Chief Adebayo Adelabu, ya jagoranci masoyansa sun koma Accord Party
- Ya ce ba zai ba al'ummar Oyo kunya ba kuma ya koma AP Ne domin cika mafarkinsa na zama gwamnan Oyo
Oyo - Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) kuma ɗan takarar gwamnan Oyo a APC, Chief Adebayo Adelabu, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar Accord Party (AC).
Daily Trust ta rahoto cewa Ɗan takarar ya ɗauki wannan matakin ne domin cika burin rayuwarsa na takarar gwamna a jihar Oyo a babban zaɓen 2023.
Adelabu, wanda ya sha ƙasa kuma ya rasa tikitin APC a hannun Sanata Teslim Folarin, ya ce AC jam'iyya ce wacce niyarsa ta neman takarar gwamna zata cika kuma mafarkinsa zai zama gaskiya.
Da yake jawabi ga dubbanin magoya bayansa kan siyasarsa ta gaba a Ibadan ranar Alhamis, Adelabu, ya ce ba bukatar sake tsokaci kan dalilin watsar da APC saboda abu ne da kowa ya sani.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Abun da ya fi komai amfani shi ne shugabanni na, magoya baya da sauran al'ummar jihar Oyo, ina mai tabbatar musu da cewa ba zan ba su kunya ba a kokarin cika burina na takarar gwamna har mafarkina ya zama gaskiya da ikon Allah."
"Na sadaukar da kaina ga wannan tafiyar siyasar domin ceto jihar mu daga jagoranci mara kyau da wasu gurɓatattun mutane na wata jam'iyya ke tafiyar wa."
Ina da manufofin 7 ga jihar Oyo - Adelabu
Da yake magana kan babban abin da zai sa a gaba da zaran ya zama gwamna, Ɗan takarar ya ce:
"A tare zamu kafa sabuwar gwamnatin zaman lafiya da cigaba a jihar mu mai albarka kan kyawawan kudirori 7 da zan sanya a gaba idan na zama zaɓaɓɓen gwamnan Oyo."
A wani labarin kuma Ana shirin zaɓen fidda gwanin APC, Babban Hadimin Buhari ya gana da Jonathan a Abuja
Kakakin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.
Shehu ya bayyana cewa dukkan su sun ji daɗi kuma sun nuna wa juna ƙauna a Otal ɗin Fraser Suites Hotel, Abuja.
Asali: Legit.ng