Tinubu ya fito da abin da ya boye tun 2015, ya fadi yadda Buhari ya nemi suyi takara tare

Tinubu ya fito da abin da ya boye tun 2015, ya fadi yadda Buhari ya nemi suyi takara tare

  • Asiwaju Bola Tinubu ya ce Muhammadu Buhari ya yi masa tayin yin takarar mataimakinsa a 2015
  • Jigon na APC ya bayyana cewa Bukola Saraki su ka yake shi, dole ya hakura saboda yana musulmi
  • Tinubu yake cewa saboda kishin APC ne ya kawo kiristocin da za su iya yi wa Buhari mataimaki

Ogun - Asiwaju Bola Tinubu wanda yana cikin ‘yan gaba-gaba a neman kujerar shugaban kasa, ya ce Muhammadu Buhari ya so su yi takara tare ne a 2015.

Punch ta ce jagoran na APC, Bola Tinubu ya bayyana wannan ne a lokacin da yake jawabi a fadar gwamnati a garin Abeokuta, jihar Ogun a ranar Alhamis.

Asiwaju Bola Tinubu ya zauna da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC yayin da ake tsammanin gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa a farkon makon gobe.

Kara karanta wannan

Takarar Tinubu, Osinbajo, Amaechi da Lawan a 2023 ta na raba kawunan na-kusa da Buhari

Wannan karo Tinubu ya bada labarin yadda ta kaya da shi da Muhammadu Buhari a zaben 2015 da yadda wasu manya su ka hana ya zama masa mataimaki.

Jawabin Tinubu da Yarbanci

“Ba ku taba jin wannan daga baki na ba kafin yau. A nan ne wurin farko da nake fadar wannan.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ina fada maku ne tsakani na da Allah Madaudakin Sarki, Buhari ya kira ni domin in zama masa mataimakin shugaban kasa.”
Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: officialasiwajubat
Asali: Facebook

Zo ka zama mataimaki na

“Ya ce saboda da farko ya dauko, Marigayi (Chuba) Okadigbo, amma duk da haka mutanen Najeriya ba su zabe shi ba.”
“Karo na biyu, ya dauko wani Ibon, (Edwin) Ume-Ezeoke, ‘yan Najeriya ba su zabe shi ba, ko Fafaroma ya dauko, ba za su zabe shi ba.”
“Sai ya ce, amma kai Bola Tinubu ka na da gwamnoni shida, ba ka taba fadi wani zabe a baya ba, zo ka zama mataimaki na.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara

- Bola Tinubu

Bola Tinubu yake cewa da harshen Yarbanci, Buhari ya san za su kai labari idan suka yi takara tare, amma sai ya ce a jira a gama kafa jam’iyya tukuna.

Lissafi ya canza da zuwan nPDP

Bayan an kafa jam’iyya, ya ce sai aka kawo mutane daga jam’iyyar PDP, (Bukola) Saraki sai ya fahimci wadanda suka zo daga PDP ba za su samu komai ba.

A cewar ‘dan siyasar, Saraki ya lura ba zai zama shugaban majalisa idan Musulmai suka zama shugaban kasa da mataimaki ba, sai ya fara yakar Tinubu.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, daga nan ne Tinubu ya bada sunayen Yemi Cardozo, Wale Edun, ko Yemi Osinbajo saboda gudun jam’iyya ta watse.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng