Sabon Bidiyo: Bola Tinubu ya yi sabuwar magana kan matakin da zai ɗauka idan ya sha ƙasa a zaɓe
- Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hasashensa kan yadda sakamakon zaben fidda gwanin APC na takarar shugaban kasa ka iya kasancewa
- Jagoran APC na ƙasa ya gaya wa magoyan bayansa su sanya ransu a inuwa yayin da ya kammala duk abinda ya dace da zasu kai shi ga nasara
- Haka nan kuma, Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ya ce idan sakamakon be masa kyau ba zai rungumi ƙaddara
Jagoran jam'iyyar All Progressive Congress wato APC na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ƙara sabuwar magana kan abin da zai yi idan ya rasa tikitin APC.
A wani Bidiyo da Jubril Gawat, mai taimaka wa gwamnan Legas ta bangaren Midiya, ya saki a shafinsa na Twitter, Tinubu a cikin yaren Yarbanci ya ce ya shirya wa zaɓen.
Ya kuma tabbatar wa magoya bayansa cewa shi zai samu nasara amma idan hakan ba ta faru ba zai rungumi ƙaddara ya koma gida.
"Idan suka kayar da ni zan rungumi kaddara na koma gida," tsohon gwamnan ya faɗa cikin yaren su na yarbawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da yake kokarin fassara kalaman Tinubi, Gawat ya rubuta cewa:
"Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce ya kammala shirya wa zaɓen fitar da ɗan takarar APC, kuma duk abin da sakamako ya nuna zai rungume shi."
"Amma ya tabbatar wa dandazon magoya bayansa a dukkan sassan ƙasar nan cewa ya yi aiki tukuru kuma kowa ya kwantar da hankalinsa."
APC ta tantance Tinubu da sauran yan takara a Abuja
Kwamitin da APC ta kafa karkashin jagorancin tsohon shugaban jam'iyya, John Oyegun, ya kammala aikinsa na tantance yan takarar shugaban kasa.
Kwamitin ya tantance jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya shaida musu irin shirye-shirye da manufofinsa da zaran ya karɓi ragamar ƙasar nan.
A wani labarin kuma Rikici ya ɓarke a Sakatariyar APC ta Abuja bayan ɗan takarar shugaban kasa ya watsa kyautar N50,000
Danbarwa ta barke tsakanin direbobi, jami'an tsaro da masoyan APC bayan gwamna Umahi ya watsa kyautar N50,000 a Abuja
Bayanai sun bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasan ya watsa kudin ne yayin da yake gab da shiga Mota a Sakatariyar APC ta ƙasa
Asali: Legit.ng