Dalla-dallar yadda aka kada kuri’u a jihohi 36 wajen tsaida ‘dan takarar shugaban kasan PDP

Dalla-dallar yadda aka kada kuri’u a jihohi 36 wajen tsaida ‘dan takarar shugaban kasan PDP

  • Bayanai sun fito a game da yadda ‘yan jam’iyyar PDP suka kada kuri’unsu a zaben tsaida gwani
  • Nyesom Wike ya samu kuri’u a kudu maso yamma da goyon bayan Seyi Makinde da Ayo Fayose

Abuja - Premium Times ta fitar da rahoto na musamman da ya nuna yadda ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP suka kada kuri’arsu a zaben makon jiya.

Jam’iyyar PDP ta tantance mutane 767 a zaben ‘dan takarar shugaban kasa. Atiku Abubakar ya samu 371, sai Nyesom Wike ya zo na biyu da kuri’a 237.

Arewa maso gabas

Janyewar Aminu Waziri Tambuwal ta sa Atiku Abubakar ya samu karin kuri’u daga jihohin Arewa ta yamma na Jigawa, Zamfara, Kebbi, Sokoto da Kaduna.

Kara karanta wannan

Mutuwar yawa: Duka Sanatoci 3 sun sha kasa a zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC a jiha 1

Nyesom Wike ya samu duk kuri’u 44 na jihar Kano a dalilin rikicin cikin gidan jam’iyya da kuma jihar Katsina, inda ya samu goyon bayan Sanata Lado Danmarke.

Arewa maso tsakiya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A Arewa maso tsakiya – Benuwai, Kogi, Kwara, Nasarawa, Neja da Filato, Atiku, Wike da Bukola Saraki ne su ka raba kuri’un da ake da su a wannnan yankin.

Saraki ya karbe Kwara, Atiku da Wike suka raba Neja. Filato da Nasarawa sun fada hannun Atiku, Wike ya mamaye Abuja, sai suka raba Benuwai da Kogi.

Arewa maso yamma

Atiku Abubakar ya samu galaba sosai a yankinsa domin ya yi nasara akalla jihohi hudu. Jaridar ta ce shi ne ya karbe Adamawa, Borno, Gombe, da jihar Yobe.

Bala Mohammed ya dauke duka kuri’un Bauchi, sai Wike da Atiku suka yi tarayya wajen samun kuri’un ‘ya ‘yan jam’iyyar daga jihar Taraba a wannan karo.

Kara karanta wannan

APC tayi zazzaga a jihar Arewa, fitattun ‘Yan Majalisa 7 za su rasa kujerunsu a 2023

'Dan takarar shugaban kasa a PDP
Wasu magoya bayan Atiku a PDP
Asali: Facebook

Kudu maso yamma

‘Yan takaran da suka zo na ukun farko suka kacancana kuri’un Ekiti, Legas, Ogun, Ondo, Osun da Oyo. Atiku Abubakar ya bada mamaki, samun kuri’un Ondo.

Gwamna Nyesom Wike ya fi karfi a Legas, Oyo da Ekiti saboda goyon bayan da ya samu daga jagororin jam’iyyar irinsu Seyi Makinde da Ayodele Fayose.

Kudu maso gabas

A cikin Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo, Atiku Abubakar ya samu nasara ne a Anambra da Imo kadai saboda gudumuwar mutanensa da na Tambuwal.

Nyesom Wike ya karbe kuri’un jihohin Abia da Enugu domin yana tare da Gwamnoni Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi. Anyim Pius Anyim ya rike Ebonyi.

Kudu maso kudu

A yankinsa, Wike ya yi nasarar samun kuri’un jihohi uku ne; Kuros Ribas, Edo, da Ribas. Rikicin cikin gida ya jawo Atiku ya gagara samun kuri’u daga Edo.

Su kuwa ‘ya ‘yan PDP na Delta da Bayelsa sun zabi Atiku Abubakar ne. Kuri’un da Udom Emmanuel ya samu sun fito ne daga jiharsa ta Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Yadda duka Sanatocin Katsina 3 su ka rasa tikitin tazarce a karkashin Jam’iyyar APC

Atiku zai dauko Emeka Ihedioha?

An ji labari cewa tunanin Emeka Ihedioha zai zama 'dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP. Ihedioha ya fito ne daga jihar Imo, a yankin kasar Ibo.

Inda Atiku Abubakar zai samu matsala da Emeka Ihedioha shi ne Peter Obi ya tsaya takarar shugaban kasa a LP daga bangaren na Kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng