2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC

2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC

  • Atiku ya nemi goyon bayan jama'ar jami'iyyar PDP gabanin babban zabe domin lallasa jam'iyyu a 2023
  • Ya bayyana haka ne kwanaki bayan lashe zaben fidda gwanin da jam'iyyar ta yi a kwanan nan a babban birnin tarayya Abuja
  • Jam'iyyun siyasa na ci gaba da sanar wadanda za su kara a zaben 2023 mai zuwa, inda suke sa ran gane Buhari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya nemi goyon bayan abokan hamayyarsa a jam’iyyar domin kayar da APC mai mulki a babban zabe mai zuwa.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan ya amshi shaidar zama dan takara na jam’iyyar a sakatariyar PDP ta kasa da ke Wadata Plaza a Abuja.

2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC
2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewar tsohon mataimakin Shugaban kasar wanda ya shafe kimanin shekaru 30 yana son zama shugaban kasar Najeriya, babbar abokiyar hamayyarsa ita ce APC amma ba wai abokan takararsa na zaben fidda gwanin PDP da aka yi ba.

Kara karanta wannan

2023: Buhari ya lissafa sharuddan da dole 'dan takarar shugabancin kasa na APC ya cika

Ya bukaci abokan takararsa da su hada karfi da karfe da shi don tunkude gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku ya bayyana nasararsa a matsayin “nasarar dukkanmu, nasarar jam’iyyarmu kuma nasarar mafi rinjayen yan Najeriya da ke shan wahala a karkashin mulki kama karya na APC.”

A yayin zaben fidda gwanin shugaban kasa na PDP wanda ya gudana a filin wasa na Moshood Abiola a ranar Asabar, Atiku ya samu kuri’u 371 wajen kayar da Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike wanda ya samu kuri’u 237.

Sauran wadanda Atiku ya kayar sune tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki wanda ya samu kuri’u 70, gwamnan Akwa Ibom, Emmanuel Udom da ya samu kuri’u 38, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da ya samu kuri’u 20 da sauransu.

2023: Kar ku ɗauka lallasa APC a zabe abu ne mai sauki, Atiku ya gargaɗi PDP

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Abin da Buhari ya fada wa gwamnonin APC kan zakulo magajinsa

A wani labarin, dan takarar PDP a zaɓen 2024l3 dake tafe, Alhaji Atiku Abubakar, ya gargaɗi mambobin jam'iyya da su koma aiki gadan-gadan kar su ɗauka, "rashin nasara da ke gaba," ga APC mai mulki abu ne mai sauki.

Da yake jawabi ga mambobin kwamitin gudanarwa NWC, jiga-jigan PDP, da masoya jim kaɗan bayan karban shaidar takarar shugaban kasa, Atiku yace abun da ya faru ba zaɓe bane illa matakin tunkarar babban zaɓe.

Ɗon haka, tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya roki kwamitin NWC da ya jawo kowa a jiki domin kwace ragamar mulki daga hannun APC, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng