Kada ka 'kakaba mana dan takaran shugaban kasa, Mataimakin Shugaban APC ga Buhari

Kada ka 'kakaba mana dan takaran shugaban kasa, Mataimakin Shugaban APC ga Buhari

  • Mataimakin shugaban jam'iyyar APC ya rubuta budaddiyar wasika wa shugaba Muhammadu Buhari
  • Mr Salihu Lukman ya shawarci Buhari yayi waiwaye kan ire-iren abinda ya faru da Gwamnonin da suka tilastawa mutane zaben wani
  • Shugaba Buhari ya bukaci gwamnoni su bari ya zabi wanda zai gajesa kamar yadda suka yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Salihu Lukman ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari kada ya tilasta musu zaben wani dan takaran kujeran shugaban kasa.

Lukman ya bayyana hakan ne a budaddiyar wasikar da ya aikewa Buhari game da zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasa karkashin APC.

A wasikar, Lukman yace:

"Mai girma shugaban kasa, ya bukaci gwamnoni da masu ruwa da tsaki su bada goyon bayan zaben wanda zai gaje ka."
"Abin damuwa shine shin kana son shugabannin jam'iyya da mambobi su zama yan kallo yayinda akwai wasu abubuwa masu muhimmanci da ka iya bata maka suna."

Kara karanta wannan

Sabuwar ɓaraka ta kunno kai a APC, mambobin NWC 2 sun buƙaci a yi wa Sanata Adamu ta-waye

"Dubi da yadda ake samun sabani tsakanin Gwamnoni da wadanda suka gajesu, da hadarin gaske kace kana son kabi wannan salo saboda za ta iya rusa dukkan nasarorinka sabanin ka bari ayi abin da zai karfafa demokradiyya a Najeriya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Salihu Lukman
Kada ka kakaba mana dan takaran shugaban kasa, Mataimakin Shugaban APC ga Buhari Hoto
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng