2023: Jam'iyyar SDP Ta Tsayar Da Gogaggen Sanata Takarar Shugaban Kasa

2023: Jam'iyyar SDP Ta Tsayar Da Gogaggen Sanata Takarar Shugaban Kasa

  • Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta zabi Sanata Ebenezer Ikeyina a matsayin dan takarar shugaban kasar ta a 2023
  • Mike Odunrinde, Shugaban Kwamitin Shirya Taron Jam'iyyar ne ya sanar da hakan a birnin tarayya Abuja bayan zaben fidda gwani
  • Odunrinde ya ce cikin daliget guda 311 da aka tantance, guda 308 sun zabi Ikeyina sai wasu biyu suka zabi wani dan takarar, kuri'a daya kuma ta lalace

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Sanata Ebenezer Ikeyina, a ranar Talata ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Shugaban Kwamitin Shirya Taron Jam'iyyar, Mike Odunrinde, wanda ya jagoranci zaben fidda gwani na jam'iyyar a Abuja, ya ce cikin daliget 311 da aka tantance, 308 sun zabi Ikeyina wanda ya wakilci Anambra ta Tsakiya a Majalisa.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Shehu Sani ya shawarci Atiku kan irin wanda ya kamata ya zaba a matsayin mataimaki

2023: Jam'iyyar SDP Ta Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasa
Jam'iyyar SDP Ta Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2023: Hoto: @nannews_ng.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu biyu sun zabi wani dan takarar daban sai kuma kuri'a guda daya an soke ta domin ta lalace.

Da ya ke yi wa daligets a jihohi 36 jawabi a wurin taron jam'iyyar a Abuja. Shugaban riko na Jam'iyyar na kasa, Supo Shonibare ya ce yan takarar jam'iyyar da ke neman kujeru daban-daban za su yi nasara a babban zaben 2023.

NAN ta rahoto cewa Shonibare ya kuma ce nan gaba za su yi taron gangami na kasa bayan kotu ta yanke hukunci kan shari'ar rikicin jam'iyyar.

A cewarsa, ana fatan dukkan mutanen bangarori biyu da ke rikici za su hallarci babban taron.

Ya jaddada cewa shugabannin jam'iyyar 'sun damu da nasarar yan takararsu.'

Ya ce:

"Ba dole ne ya faru cikin gaggawa ba amma muna fatan za mu yi nasara. Kuma ina tabbatar muku ba za mu gajiya ba."

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

Buratai: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya Ya Ba Wa APC Gudunmawar Motar Kamfen Ƙirar Najeriya

A wani rahoton, tsohon babban hafsan sojin kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai; Babban Kwamishinan Najeriya a Jamhuriyar Zambia, Nwanebike Oghi da kuma wasu jakadu na musamman a ranar Laraba sun bai wa shugabancin jam’iyyar APC kyautar motoci kirar bas mai daukar mutum 18.

Farar motar, wacce kamfanin Innoson Motors ne ya kerata sabuwa ce kuma a jikinta a rubuta “Jakadu na musamman ne su ka bayar da kyautarta,” The Punch ta ruwaito.

Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164