2023: Namadi Sambo, Sule Lamido da wasu jiga-jigan PDP a arewa sun ziyarci Atiku Abubakar
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya karbi bakuncin jiga-jigan PDP a arewa
- Atiku ya bayyana cewa sun tattauna yadda za su karfafa hadin kai a cikin jam'iyyarsu gabannin babban zabe mai zuwa
- Wadanda suka kai masa ziyarar sune Namadi Sambo, Attahiru Bafarawa, Sule Lamido da Mohammed Hayatu-Deen
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya gana da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar daga yankin arewa a ranar Talata, 31 ga watan Mayu.
Daga cikin wadanda suka ziyarci Atiku akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.
Hakazalika, abokin hamayyarsa wajen fafutukar tikitin jam’iyyar a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na 2023, Mohammed Hayatu-Deen na cikin tawagar da suka ziyarce shi.
Jerin gwamnoni 7 da ke neman matsuguni a majalisar dattawa ta 10 bayan sun lashe tikitin takara a jam’iyyunsu
Atiku ne ya sanar da labarin haduwar tasu a wata wallafa da ya yi a shafinsa na twitter mai suna @atiku.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, sun ziyarce shi ne domin karfafa hadin kai a jam’iyyarsu mai adawa a kasar.
Ya rubuta:
“Na ji dadin kasancewa mai masaukin baki mai girma Namadi Sambo, mai girma Sule Lamido, mai girma Attahiru Bafarawa da Alh Mohammed Hayatu-Deen.
“Ziyarar taya murnar ya bamu damar tattauna yadda za mu karfafa hadin kan jam’iyyarmu, PDP da sauransu - AA.”
An sake maka Atiku Abubakar a kotu, ana neman haramta masa tsayawa takara har abada
A wani labarin, mun ji cewa wani Lauya da ke aiki a Abuja, Johnmary Jideobi, ya roki babban kotun tarayya ta haramtawa Atiku Abubakar neman kujerar shugaban kasa.
Premium Times ta ce Johnmary Jideobi yana kalubalantar zama ‘dan kasar Atiku Abubakar wanda ya yi shekaru takwas yana mataimakin shugaban kasa.
A karar da ya shigar a kotun da ke zama a garin Abuja, Jideobi ya hada da Atiku Abubakar, jam’iyyar PDP, hukumar INEC da babban lauyan gwamnati.
Asali: Legit.ng