APC tayi zazzaga a jihar Arewa, fitattun ‘Yan Majalisa 18 za su rasa kujerunsu a 2023
- A cikin duka Sanatocin Jigawa, babu wanda zai koma kan kujerarsa a karkashin jam’iyyar APC
- Shi ma Hon. Muhammad Gudaji Kazaure da wasu mutane uku ba za su koma majalisar tarayya ba
- Mataimakin Gwamna Umar Namadi ya doke Sanatan Arewa maso yamma, zai yi takarar Gwamna
Jigawa - Siyasar jihar Jigawa ta zo da wani sabon salo a zaben 2023 inda aka ji Sanatoci uku masu-ci sun gagara samun tikitin sake neman takara a APC.
Jaridar Sahelian Times ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu 2022, wanda ya tabbatar da cewa duk Sanatocin Jigawa sun rasa tikitin takara.
Sanata Ibrahim Hassan Hadejia da Sanata Sabo Muhammad Nakudu sun yi biyu-babu yayin da suka yi watsi da kujerunsu, suka je neman takarar gwamna.
Shi kuma Sanata Dandali Sankara ya gagara samun tikitin tazarce a karkashin jam’iyyar APC.
Ibrahim Hassan Hadejia wanda ya rike kujerar Mataimakin gwamnan Jigawa ba zai zama ‘dan takarar APC na shiyyar Jigawa ta Arewa maso gabas a 2023 ba.
Mataimakin Gwamna zai gaji Badaru
Mataimakin gwamna, Umar Namadi ya zama ‘dan takaran Gwamna a APC, ya doke Sanatan Arewa maso yamma, Sabo Muhammad Nakudu da kuri’a 1220.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gudaji sun sha kashi
A zaben majalisar tarayya kuwa, Hon. Muktar Muhammed Zanna ya tika Muhammad Gudaji Kazaure da kasa a mazabar Kazaure/Yankwashi/Gwiwa/Roni.
Hon. Gudaji Kazaure wanda ya je majalisa a 2015 yana rigima da Gwamna Muhammad Badaru, ana rade-radin zai sauya sheka zuwa jam’iyyar nan ta NNPP.
Haka zalika ‘yan majalisar wakilan tarayya da ke kan kujerunsul Hon. Ado Sani Kiri, Hon. Shitu Galambi, da Hon. Fagen Gawo duk ba su iya samun tikiti ba.
Wadanda za su yi takarar majalisa daga Jigawa a APC su ne: Makki Abubakar Elleman, Magaji Da’u Aliyu, Ibrahim Abdullahi Kemba, da kuma Abubakar Fulata.
Ragowar ‘yan takaran su ne: Yusuf Sa’idu Miga, Isah Idris Gwaram, Sa’ad Wada Taura, Aminu Kanta Babura. Sai Nazifi Sani da shi Muktar Muhammed Zanna.
'Yan majalisar dokoki
Rade-radi na yawo cewa akwai 'yan majalisar dokoki fiye da 10 da ba za su yi takara a APC ba.
'Yan majalisun sun hada da Abdulrahman Alkasim, Musa Sule Dutse, Hassan Alto Roni, Musa Sulaiman, Bala Hamza Gada, da kuma Kabiru Isa Babura.
Idan labarin ya tabbata, ragowar su ne: Hon Kais Abdallah, Hon Usman Haladu Killer KANYA, Hon Na Laure. Hon Lawan Garba, a karshe sai; Ibrahim Kadeta.
Tinubu ta hakura da 2023
A siyasar Legas, an samu labari Oluremi Tinubu za ta hakura da sake zama Sanata tun da Mai gidanta yana neman shugaban kasar Najeriya a jam'iyyar APC.
Idan Tinubu ya yi nasarar samun tikitin APC, ya ci babban zabe, Tinubu za ta zama Uwargidar shugaban Najeriya a 2023 kamar yadda ta zama a jihar Legas.
Asali: Legit.ng