Zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP: Jerin yan takarar da basu samu kuri’a ko daya ba
Abuja - Babbar jam’iyyar adawar kasar ta Peoples Democratic Party (PDP) ta zabi dan takararta na shugaban kasa na babban zaben 2023 a ranar Asabar, 28 ga watan Mayu.
Kafin zaben, yan takara 17 ne suka biya naira miliyan 50 na fom din takara.
Sai dai, an hana yan takara biyu shiga tseren yayinda wasu uku, Mohammed Hayatu-Deen, Aminu Tambuwal da Dr Nwachukwu Anakwenze suka janye daga tseren, inda mutum 12 suka fafata a tsakaninsu.
Yayin da Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto ya janyewa Atiku, Anakwenze ya marawa Gwamna Wike baya bayan fitarsa daga tseren.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe zaben da kuri’u 371 yayin da Gwamna Nyesom Wike ya zo na biyu da kuri’u 237.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya samu kuri’u 70; Bala Mohammed, gwamnan Bauchi, kuri'u 20; Udom Emmanuel, gwamnan Akwa Ibom, kuri'u 38; Pius Anyim kuri’u 14, Olivia Tariela (mace daya tilo da ta tsaya takara), kuri’a 1 da Sam Ohuabunwa, kuri’a 1.
Sai dai kuma, sauran yan takarar da aka fafata da su har zuwa karshe basu samu kuri’a ko daya ba.
Daga cikin wadanda basu samu kuri’a ko daya ba harda Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti.
Jihar Ekiti inda daga nan ne Fayose ya fito tana da deleget 16 amma kuma bai samu kuri’a ko guda ba.
Zaben fidda gwanin PDP: Yan takarar shugaban kasa da basu samu kuri’a ko daya ba
- Ayo Fayose
- Dele Momodu, dan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation
- Charles Okwudili, lauya
- Chikwendu Kalu
Cikakken sakamako: Yadda Atiku ya lallasa Wike, Saraki da sauransu wajen samun tikitin shugaban kasa na PDP
EFCC ta yi ram da tsohon gwamna kan zargin hannu a damfarar N80b ta dakataccen AGF
A wani labarin, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta damke tsohon gwamna Abdulaziz Yari kan binciken da hukumar ke yi game da kudaden da ake zargin akanta janar Ahmed Idris da kwashewa.
Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, an kama shi ne a yammacin Lahadi a gidansa da ke Abuja, kwanaki kadan bayan da yayi nasarar samun tikitin takarar kujerar sanata na Zamfara ta yamma wanda za a yi a shekara ta gaba. Ya yi nasara babu abokin hamayya, Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng