Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta ɗage zaɓen fidda dan takarar shugaban ƙasa
- A ranar Jumu'a hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta amince da karin wa'adin miƙa jerin sunayen yan takarar jam'iyyu
- Hakan ya ba jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan damar ɗage taronta na zaɓen fidda gwani ɗaga yan takarar shugaban kasa
- Maimakon ranar 29 da 30 ga watan Mayu, APC ta maida zaɓen zuwa ranar 6,7 da kuma 8 ga watan Yuni
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Jam'iyyar All Progressive Congress wato APC ta sake ɗaga zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa wanda ta tsara gudanarwa ranar 29 da 30 ga watan Mayu, 2022.
A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta hannun sakataren tsare-tsare, Felix Morka, ta ce ta yi haka ne biyo bayan ƙara wa'adin miƙa sunayen yan takara da INEC ta yi.
APC ta ce maimakon ranakun da ta tsara, ta ɗage zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa zuwa ranakun 6,7 da kuma 8 ga watan Yuni, 2022.
Jam'iyya mai mulki ta rubuta a shafinta na Tuwita cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Biyo bayan matakin INEC na kara wa'adin miƙa sunayen yan takara, jam'iyyar APC ta ɗage taronta na musamman na zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa daga 29 da 30 ga Mayu zuwa 6,7 da 8 ga watan Yuni, 2022."
INEC ta ɗage wa'adin miƙa sunayen yan takara
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ƙara wa'adin karɓan sunayen yan takara jam'iyyu da kwana shida kan wa'adin ta sanya tun farko.
Hukumar ta ɗauki wannan matakin ne a wurin taronta da jagorancin jam'iyyun siyasa 18 masu rijista a Hedkwatar INEC ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Kwamishinan yaɗa labarai na INEC, Festus Okoye, ya ce:
"INEC ta yanke shawarar amincewa da koken jam'iyyun siyasa duba da kwana shida ba zai rusa ayyukan da ta shirya na gaba ba."
A halin yanzun, babban jam'iyyar hamayya PDP ta fara gudanar da harkokin zaɓen fitar da gwani daga yan takarar shugaban ƙasa, wanda ta tsara yi ranar Asabar (yau) da Lahadi.
A wani labarin kuma Wani Ɗan majalisar jiha ya sauka sheƙa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC a Kano
Wani ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu a Kano ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.
Honorabul Muazzam El-Yakuba, ya tabbatar da sauya shekarsa ne a wata takarda da ya aike wa majalisar dokokin jihar Kano.
Asali: Legit.ng