Da Dumi-Dumi: Mako ɗaya bayan Murabus, Ministan Buhari ya lashe tikitin gwamna a APC
- Tsohon ministan haƙar ma'adanai da ƙarafa, Uche Ogah, bai rasa baki ɗaya ba bayan ya yi murabus daga kujerarsa
- A ranar 27 ga watan Mayu, 2022 aka bayyana Ogah a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar Abia na APC
- Daga cikin kuri'u 195,801 da aka kaɗa a zaɓen, Ogah ya samu kuri'u 141,952 kuma shi baturen zaɓe ya sanar ya lashe zaɓe
Abia - Tsohon ministan haƙar ma'adai da cigaban ƙarafa da ya sauka, Uche Ogah, ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar Abia na jam'iyyar APC.
Ogah, bayan gudanar da zaben fitar da gwani ta hanyar ƙato bayan ƙato ranar Jumu'a 27 ga watan Mayu, 2022, ya samu kuri'u 141,952 daga cikin kuri'u 195,801da aka kaɗa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Baturen zaɓen jihar, Perfect Okorie, ya bayyana tsohon Ministan a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma a cewarsa an gudanar da zaɓe mai inganci.
Ogah ya yi godiya bayan samun nasara
Da yake jawabi bayan bayyana sakamako, Ogah ya gode wa mambobin jam'iyyar APC da suka kaɗa kuri'unsu bisa yarda da shi, inda ya ƙara da cewa ba zai ba su kunya ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ɗan takarar gwamnan Abia karkashin APC ya ce ya sadaukar nasarar da ya samu ga Allah, inda ya ƙara da cewa yana da kwarin guiwar zai samu nasara a zaɓen 2023.
A kwanakin baya, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci ministocinsa da sauran naɗe-naɗensa waɗan da ke da burin tsayawa takara su yi murabus.
Wasu daga cikin ministoci sun bi umarnin shugaban sun aje aiki amma wasu kuma sai suka janye daga takarar da suka yi nufin yi a 2023.
A wani labarin kuma Wani Ɗan majalisar jiha ya sauka sheƙa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC a Kano
Wani ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu a Kano ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.
Honorabul Muazzam El-Yakuba, ya tabbatar da sauya shekarsa ne a wata takarda da ya aike wa majalisar dokokin jihar Kano.
Asali: Legit.ng