Da Dumi-Dumi: Ɗan Ministan Buhari ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC
- A kokarinsa na sake komawa majalisa karo na uku, ɗan ministan yada labarai da Al'adu ya sha ƙasa a zaben fid da gwanin APC
- Folajimi Mohammed, ya rasa tikitin zarcewa kan kujerar mamba mai wakiltar mazaɓar Ikeja 1 a majalisar dokokin jihar Legas
- Jami'an tsaro sun tsaurara matakan tsaro yayin gudanar da zaɓen yau Jumu'a 27 ga watan Mayu 2022
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagos - Folajimi Mohammed, ɗan ministan yada labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya rasa tikitin wakiltar mazaɓar Ikeja 1 a majalisar dokokin jihar Legas.
Ɗan ministan, wanda yanzu haka ya ke kan kujerar ɗan majalisar jiha a karo na biyu ya gaza samun tikitin ta zarce, inda ya sha kaye da zaɓen fid da gwanin jam'iyyar APC.
Daily Trust ta rahoto cewa a ranar Jumu'a (Yau) 27 ga watan Mayu, na shekarar 2022, jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fitar da yan takarar ta a jihar Legas.
Siyasar Kano: Wani ɗan majalisa tare da dandazon magoya bayansa sun fice daga NNPP ta Kwankwaso, sun koma APC
Yayin da Falajimi Muhammed ya samu kuri'u 9 a zaɓen fitar da ɗan takarar, shi kuma abokin karawarsa, Seyi Lawal ya samu kuri'u 15.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Magoya baya da masoyan Lawal sun ɓarke da murna bayan shugaban kwamitin zaɓen, Ewuoso Olamide, ya ayyana mai gidansu a matsayin wanda ya lashe zabe.
Yadda zaɓen ya gudana
Premium times ta ruwaito cewa zaɓen fidda gwanin, wanda aka gudanar a makarantar Firamaren St Peters Anglican, ya kammalu ne karƙashin tsaauraran matakan tsaro.
Haka nan, wakilan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) sun halarci wurin domin sa ido kan abin da ke wakana.
Yan takara 9 ne suka fafata a zaɓen waɗan sa suka haɗa da Messrs Mohammed, Lawal, Ladapo Oyebiyi, Ismail Balogun, Taofeek Olorunfunmi, Olabode Akerele, Adegboyega Kuku, Bode Tawak, da kuma Adesipe Adebiyi.
Da yake sanar da sakamakon, shugaban kwamitin zaben yace Mista Lawal ya samu kuri'u 15, hakan ya bashi damar lallasa Mista Muhammed, wanda ya samu kuri'u 9.
A wani labarin kuma Wani Ɗan majalisar jiha ya sauka sheƙa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC a Kano
Wani ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu a Kano ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.
Honorabul Muazzam El-Yakuba, ya tabbatar da sauya shekarsa ne a wata takarda da ya aike wa majalisar dokokin jihar Kano.
Asali: Legit.ng