Sokoto: Ƴan Takarar APC Sun Fice Daga Wurin Zaɓen Fidda Gwani a Fusace Bayan Ɗaukewar Wutar Lantarki

Sokoto: Ƴan Takarar APC Sun Fice Daga Wurin Zaɓen Fidda Gwani a Fusace Bayan Ɗaukewar Wutar Lantarki

  • Akalla ‘yan takara uku cikin biyar na gwamnan Jihar Sokoto na jam’iyyar APC ne su ka fita daga cikin ofishin jam’iyyar cikin fushi, yayin da ake tsaka da zaben fidda gwani
  • Wannan ya biyo bayan rashin wutar lantarki a ofishin sakamakon karewar man fetur a injin din da ke samar da wutar wanda ya sa aka dinga zama a haka kusan sa’a daya
  • An ci gaba da amfani da tocila wurin yin zaben wanda hakan ya hassala ‘yan takarar da su ka nemi a jira sai wuta ta dawo, daga nan su ka dinga fita daga wurin daya bayan daya

Sokoto - Yayin da ake tsaka da zaben fidda gwanin jam’iyyar APC a Jihar Sokoto, akalla ‘yan takarar gwamna guda uku cikin guda 5 ne su ka bar wurin zaben, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi garkuwa da 'yar takarar APC ana tsaka da zaben fidda gwani

Hakan ya biyo bayan rashin wutar lantarki a babban ofishin jam’iyyar na jihar bayan man fetur din injin da ke samar da wutar ya kare.

Sokoto: Ƴan Takarar APC Sun Fice Daga Wurin Zaɓen Fidda Gwani a Fusace Bayan Ɗaukewar Wutar Lantarki
'Yan Takarar APC Sun Fice Daga Wurin Zaɓen Fidda Gwani a Fusace Bayan Ɗaukewar Wutar Lantarki a Sokoto. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wakilin The Punch ya bayyana yadda lamarin ya kai kusan sa’a daya inda wasu ‘yan takarar su ka nemi a dakata da zaben har a dawo da wuta amma aka ki sauraronsu.

An ci gaba da yin zaben yayin da ake amfani da tocila wanda hakan ya bata musu rai su ka fara barin ofishin cike da fushi.

Cikin ‘yan takarar da su ka bar ofishin akwai tsohon ministan sufuri, Yusuf Suleiman, tsohon Jakadan Najeriya a Jordan, Faruk Yabo da Abubakar Gumbi.

‘Yan daba sun yi yunkurin kai musu farmaki

Akwai wasu ‘yan bangar siyasar da ake zargin su na bayan shugaban jam’iyyar na jihar, Aliyu Wamakko da su ka yi yunkurin kai wa ‘yan takarar farmaki yayin da su ke kokarin barin harabar ofishin.

Kara karanta wannan

An samu matsala: 'Yan bindiga sun harbe deliget 3 na zaben gwamnan PDP a jihar Arewa

The Punch ta tattaro cewa ‘yan bangar sun kai wa jami’an tsaron harabar farmaki yayin da su ke fadin “Sai Aluu,” wakar da masoyan Wamakko su ke yawan yi masa a jihar.

An ci gaba da yin zaben fidda gwanin da aka fara ana saura mintoci kadan 11 na dare ta yi har zuwa karfe 6:30 na safiyar Juma’a.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164