Da duminsa: Aisha Binani ta lallasa mazaje biyar, ta lashe zaben fidda gwanin APC a Yola
- Sanata Aishatu Binani ta zama Zakarar gwajin dafi a siyasar jihar Adamawa da ma Arewa gaba daya
- Yar majalisar dattawar ta kayar da manyan jiga-jigan siyasa biyar a jhar dake Arewa maso gabas
- Yanzu za ta shiga damben kuri'u da Gwamnan jihar Mai ci, Umar Ahmadu Fintiri a zaben 2023
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Adamawa - Sanata Aishatu Binani ta lallasa gardawa biyar a zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa.
Binani ta zama mace ta farko da ta lashe zaben fidda gwanin APC a jihar Adamawa
Aishatu Binani wacce yanzu haka Sanata ce mai wakiltar Adamawa ta tsakiya ta lallasa tsohon gwamnan jihar, Jibrilla Bindow da tsohon Shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu.
Hakazalika cikin wadanda ta lallasa akwai dan majalisar wakilai, AbdulRazaq Namdas, Wafari Theman da Umar Mustapha.
Shugaban kwamitin zaben, Gamba Lawan, yayin sanar da sakamakon ya bayyana cewa Binani ta samu kuri'u 430, inda Nuhu Ribadu ya samu 288.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa Binani ta rabawa kowani Deleget Naira milyan daya bayan kyaututtuka daban-daban da tayi.
An fara zaben ne misalin karfe 11:30 na daren Alhamis kuma aka kammala misalin karfe 8:44 na safiyar Juma'a.
Adadin kuri'un da kowani dan takara ya samu:
Sunan dan takara | Adadin kuri'unsa |
Aisha Binani | 430 |
Nuhu Ribadu | 288 |
Jibrilla Bindow | 103 |
Abdulrazak Namdas | 94 |
Umar Mustapha | 39 |
Wafari Theman | 21 |
An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna
An damke wasu yan siyasa biyu da ake zargin masu yiwa Sanata Aisha Binani yakin neman zabe ne suna rabawa Deleget makudan kudi a jihar Adamawa.
Aisha Binani, wacce Sanata ce mai wakiltar mazabar Adamawa ta tsakiya a yanzu tana neman zama gwamnan jihar.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Sanatar ta yiwa Deleget alkawarin basu ninkin duk kudin da sauran yan takara suka basu.
An tattaro cewa sun fara tuntubar Deleget kenan don raba musu kudi yayinda aka fara zaben fidda gwanin dake gudana da daren nan.
Asali: Legit.ng