Bidiyon yadda Kakakin majalisa ya duƙa kan guiwa yana gode wa gwamna bayan lashe zaɓen fidda gwanin PDP
- An hangi kakakin majalisar dokokin jihar Delta a wani bidiyo ya duƙa kan guiwarsa yana mai godiya ga gwamna Okowa
- Hakan ya biyo bayan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwanin PDP wanda ya gudana ranar Laraba, 25 ga watan Mayu
- Jam'iyyar PDP ta zaɓi yan takarar gwamna da zasu fafata a babban zaɓen 2023 a mafi yawan jihohin Najeriya
Delta - Kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya duƙa kan guiwowinsa a gaban gwamna Ifeanyi Okowa, domin ya gode masa.
Daily Trust ta ruwaito cewa Kakakin majalisar ya yi haka ne bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin PDP ya zama ɗan takarar gwamna a 2023.
A ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, jam'iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fitar da yan takarar da zasu fafata a zaɓen gwamna da ke tafe.
Yayin zaɓen a jihar Delta, Oborevwori, ya samu kuri'u 597 daga cikin kuri'u 824 da Deleget suka kaɗa a wurin zaɓen.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kalli Bidiyon anan
A zaɓen fidda gwani da jam'iyyar PDP ta gudanar jiya Laraba, ta fitar da yan takarar da zasu kare martabarta a babban zaɓen 2023 a kusan dukkanin jihohin Najeriya.
Sai dai jam'iyyar ta ɗage wasu zaɓukan zuwa yau Alhamis, bisa wasu dalilin na tsaro da yuwuwar ta da zaune tsaye.
Jihar Katsina a arewa maso yamma da jihar Neja a arewa ta tsakiya, yau Alhamis ake gudanar da zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna ƙarƙashin PDP.
A wani labarin kuma Batanci ga Annabi: Sabuwar matsala ta kunno kai a shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara
Mai magana da yawun Kotunan Musulunci a jihar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya sanar da ɗage zaman shari'ar Sheikh Abduljabbar.
Ya ce ba za'a samu damar zaman Kotun ba yau saboda Alkalin da ke jagorantar Shari'ar ba shi da lafiya, sai 2 ga watan Yuni, 2022.
Asali: Legit.ng