Bayan shekaru 30, NYSC ta tona asirin Sanata, an gano ba ta karasa bautar kasa ba

Bayan shekaru 30, NYSC ta tona asirin Sanata, an gano ba ta karasa bautar kasa ba

  • A shekarar 1982/83 aka tura Stella Adaeze Oduah zuwa jihar Legas domin tayi wa Najeriya hidima
  • Sanata Stella Adaeze Oduah ba ta kammala wannan bautar ba, amma sai ga shi tana da satifiket
  • Hukumar NYSC ta bayyana cewa babu yadda za ayi tsohuwar Ministar ta samu takardar shaida

Abuja - Hukumar NYSC mai kula da hidimar kasa ta ce tsohuwar Ministar harkokin jirgin sama, Sanata Stella Oduah ba ta kammala bautar kasar ta ba.

A wata wasika da Darekta Janar ya aika, Daily Trust ta fahimci hukumar ta tabbatar da Stella Oduah ta yi watsi da aikin hidimar kasarta a 1982/19383.

Shugaban hukumar NYSC ya rubuto takarda ne domin amsa tambayar da wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP suka yi, suna neman jin gaskiyar lamarin Sanatar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan janyewa daga takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fice daga PDP

‘Ya ‘yan jam’iyyar a Arewacin Anambra su na da ja a kan takardun Sanata Odua.

A amsar da NYSC ta bada, ta ce Oduah na cikin wadanda aka aika zuwa Legas domin yi wa kasa hidima a shekarar 1982/83, amma ba ta gama bautar ba.

Jaridar ta ce Eddy Megwa ne ya sa hannu a wannan takarda mai lamba NYSC/DHQ/PPRU/783/ VILIII a madadin Darekta Janar na hukumar NYSC na kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sen. Stella Oduah
Sanatar Anambra ta Arewa Stella Oduah Hoto: Legit

“Abin da hakan yake nufi shi ne ba ta cancanci a ba ta takardar shaidar yi wa kasa hidima ba.”

- Eddy Megwa

Allura ta tona garma

A shekarar 2014, tsohuwar Ministar ta taba kai kara wajen ‘yan sanda, inda ta ce takardunta sun bace da ta ke hanyar zuwa Abuja daga garin Akili a Ogboru.

Rahoton ya ce a wancan lokaci, Stella Oduah ta sa shaidar NYSC a cikin takardunta da suka bace.

Kara karanta wannan

Mun gano take-taken, Goodluck Jonathan ne 'Dan takarar Buhari a zaben 2023 inji Kungiyar APC

Ganin zabe ya karaso, ‘yan jam’iyyar PDP suka bukaci shugaban hukumar ya fito da satifiket din ainihi da aka ba Stella Adaeze Oduah tun a shekarar 1983.

Haka zalika an hurowa jam’iyyar PDP wuta cewa ana bukatar ganin takardar Sanatar, ko kuma a hana ta shiga takarar majalisar dattawa da ta ke shirin yi.

Babban lauya Ebun-Olu Adegboruwa SAN ya bada shawarar a tsige Oduah, a hukunta ta. Sannan a karbe albashin da ta karba da ta ke Minista, a hana ta takara.

Kotu ta wanke Kemi Adeosun

A shekarar 2021 ne aka ji labari cewa bayan watanni ana zargin ta da laifi, kotu ta wanke Kemi Adeosun a Abuja. A dalilin badakalar ne ta ajiye aikinta a 2018.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ce tsohuwar Ministar kudin ta na da dalilai gamsassu da suka sa bata yi bautar kasa ba domin shekarunta sun wuce.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Muka Yi Dirar Mikiya a Gidan Okorocha, EFCC Ta Magantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel