Bayan shekaru 30, NYSC ta tona asirin Sanata, an gano ba ta karasa bautar kasa ba
- A shekarar 1982/83 aka tura Stella Adaeze Oduah zuwa jihar Legas domin tayi wa Najeriya hidima
- Sanata Stella Adaeze Oduah ba ta kammala wannan bautar ba, amma sai ga shi tana da satifiket
- Hukumar NYSC ta bayyana cewa babu yadda za ayi tsohuwar Ministar ta samu takardar shaida
Abuja - Hukumar NYSC mai kula da hidimar kasa ta ce tsohuwar Ministar harkokin jirgin sama, Sanata Stella Oduah ba ta kammala bautar kasar ta ba.
A wata wasika da Darekta Janar ya aika, Daily Trust ta fahimci hukumar ta tabbatar da Stella Oduah ta yi watsi da aikin hidimar kasarta a 1982/19383.
Shugaban hukumar NYSC ya rubuto takarda ne domin amsa tambayar da wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP suka yi, suna neman jin gaskiyar lamarin Sanatar.
‘Ya ‘yan jam’iyyar a Arewacin Anambra su na da ja a kan takardun Sanata Odua.
A amsar da NYSC ta bada, ta ce Oduah na cikin wadanda aka aika zuwa Legas domin yi wa kasa hidima a shekarar 1982/83, amma ba ta gama bautar ba.
Jaridar ta ce Eddy Megwa ne ya sa hannu a wannan takarda mai lamba NYSC/DHQ/PPRU/783/ VILIII a madadin Darekta Janar na hukumar NYSC na kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Abin da hakan yake nufi shi ne ba ta cancanci a ba ta takardar shaidar yi wa kasa hidima ba.”
- Eddy Megwa
Allura ta tona garma
A shekarar 2014, tsohuwar Ministar ta taba kai kara wajen ‘yan sanda, inda ta ce takardunta sun bace da ta ke hanyar zuwa Abuja daga garin Akili a Ogboru.
Rahoton ya ce a wancan lokaci, Stella Oduah ta sa shaidar NYSC a cikin takardunta da suka bace.
Ganin zabe ya karaso, ‘yan jam’iyyar PDP suka bukaci shugaban hukumar ya fito da satifiket din ainihi da aka ba Stella Adaeze Oduah tun a shekarar 1983.
Haka zalika an hurowa jam’iyyar PDP wuta cewa ana bukatar ganin takardar Sanatar, ko kuma a hana ta shiga takarar majalisar dattawa da ta ke shirin yi.
Babban lauya Ebun-Olu Adegboruwa SAN ya bada shawarar a tsige Oduah, a hukunta ta. Sannan a karbe albashin da ta karba da ta ke Minista, a hana ta takara.
Kotu ta wanke Kemi Adeosun
A shekarar 2021 ne aka ji labari cewa bayan watanni ana zargin ta da laifi, kotu ta wanke Kemi Adeosun a Abuja. A dalilin badakalar ne ta ajiye aikinta a 2018.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ce tsohuwar Ministar kudin ta na da dalilai gamsassu da suka sa bata yi bautar kasa ba domin shekarunta sun wuce.
Asali: Legit.ng