Buratai: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya Ya Ba Wa APC Gudunmawar Motar Kamfen Ƙirar Najeriya
- Tsohon shugaban rundunar sojin kasan Najeriya kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai da wasu jakadu na musamman sun bayar da kyautar mota kirar bas mai daukar mutane 18 don kamfen ga APC
- Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar APC da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu
- Sun ce sun san cewa a halin yanzu jam’iyyar ta na fama da kai-komo kuma su na bukatar abin hawa, hakan ya sa su ka siya farar motar ta kamfanin Innoson don tallafawa jam’iyyar
Abuja - Tsohon babban hafsan sojin kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai; Babban Kwamishinan Najeriya a Jamhuriyar Zambia, Nwanebike Oghi da kuma wasu jakadu na musamman a ranar Laraba sun bai wa shugabancin jam’iyyar APC kyautar motoci kirar bas mai daukar mutum 18.
APC Ta Fara Tantance Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a Yau Talata Yayin Da Jami'an EFCC Suka Mamaye Gidan Okorocha
Farar motar, wacce kamfanin Innoson Motors ne ya kerata sabuwa ce kuma a jikinta a rubuta “Jakadu na musamman ne su ka bayar da kyautarta,” The Punch ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.
Yayin da Oghi ya bayyana dalilin bayar da kyautar motar, ya ce musamman saboda kamfen din zaben da ke matsowa ne.
Jakadan ya ce burinsu shi ne ci gaba da samar da shugaban kasar da zai ciyar da kasa gaba
A cewarsa:
“Mun san cewa a halin da ake ciki yanzu, ana ta shirye-shiryen zabe kuma akwai zirga-zirga. Hakan ya sa mu ka siyo tamu motar wacce za ta dauki mutane 18 kirar Innoson don tallafawa jam’iyyar.
Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba
“Za mu dawo gida, a matsayinmu na ‘yan jam’iyya, mun zo nan ne don taya sabbin Shugabannin Kwamitin Ayyuka ta Kasa, NWC, wacce Sanata Abdullahi Adamu ke jagoranta murna.”
Yayin da aka tambaye shi burinsu baya ga shirye-shiryen zabe, bisa ruwayar The Punch, jakadan cewa ya yi:
“Burinmu a bayyane ya ke, mu ci gaba da samar da shugabannin kasa don ciyar da Najeriya gaba.”
2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa
A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.
Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.
Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.
A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.
Asali: Legit.ng