Da duminsa: An lallasa Dino Melaye a zaben fidda gwani, ya bayyana musabbabin hakan
- Abokin adawar Sanata Dino Malaye, Hon. Tajudeen Yusuf ya ruguza masa lissafin dawowa majalisar jiha a shekarar 2023
- Dan siyasan ya bai wa Melaye kashi a zaben fidda gwani na kujerar sanata a PDP na yammacin Kogi da kuri'u 163
- A martaninsa, Sanata Malaye ya taya TJ Yusuf murna, amma ya zargi cewa akwai wata kullalliyar da aka shirya mishi inda aka hade masa kai
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kogi - Sanata Dino Malaye na jihar Kogi ya sha kaye a zaben fidda gwani na kujerar sanatan yammacin Kogi a jam'iyyar adawa (PDP) ga abokin adawarsa Hon. Tajudeen Yusuf.
Dino ya samu kuri'u 99, yayin da Hon. Tajudeen Yusuf, wanda a halin yanzu yake wakiltar mazabar Kabba/Bunu Ijumu, wanda ya samu kuri'u 163, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng ta tattaro yadda TJ Yusuf, wanda ya yi wakilcin majalisar dattawa so uku, ya kara da dino Malaye a daren Litinin, 23 ga watan Mayu, inda dukansu suka tashi da kuri'u 88; wanda ya yi sanadin sake zaben fidda gwanin.
Yadda TJ Yusuf ya lashe zaben fidda gwanin da a ka sake a ranar Talata, 24 ga watan Mayu, har ya kashe kusan duk kuri'un
Yayin da TJ Yusuf yake goyon bayan Nyesom Wike a jihar a matsayin 'dan takarar shugaban kasa, Dino Malaye ya goyi bayan Attiku Abubakar, hakan yasa wasan ya zama tsakanin jiga-jigai 'yan takarar shugaban kasa guda biyun masu fadi a ji na jam'iyyar.
Hakan yasa TJ Yusuf ya yi nasarar samun goyon baya daga tsagin tsohon Ibrahim Idris wanda ya samu kuri'u 72 a zaben fidda gwanin da a ka fara yi a daren Litinin.
Kuri'un Sam Aro ne suka canza bakin zaren zaben tare da taimakawa TJ Yusuf gami da dakile burin Dino Malaye na fitowa Sanata a shekarar 2023.
Dino Melaye ya yi martani
Dino Malaye ya yi martani gami da zargin "An hade masa kai".
Ba tare da kasa a guiwa ba, ya taya TJ Yusuf murnar nasarar da ya samu a zaben fidda gwani.
Malaye ya rubuta a shafinsa na Facebook: "An yi zaben fidda gwanin kuma an yi nasara. Ina taya Hon. TJ Yusuf murna sannan ina godiya ga wadanda su ka zabe ni a karo na farko da na biyu. Hade min kai da aka yi ba ya misaltuwa, amma ina godiya ga Ubangiji. Ubangiji ya yi muku albarka baki daya. SDM"
Asali: Legit.ng