Janar Buratai ya burma siyasa, ya bayyana wanda yake goyon baya ya karbi mulki a APC

Janar Buratai ya burma siyasa, ya bayyana wanda yake goyon baya ya karbi mulki a APC

  • Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana dalilin da ya sa yake goyon bayan takarar Rotimi Amaechi
  • Tukur Yusuf Buratai yana ganin tsohon Ministan ya fi dacewa ya karbi shugabanci a zaben 2023
  • Tsohon hafsun sojojin ya ce Amaechi ya nuna irin kokarinsa a duk mukaman da ya rike a tarihi

Bauchi - Tukur Yusuf Buratai wanda ya taba rike shugaban hafsun sojojin kasa ya yabi Rotimi Amaechi, wanda yake neman tikitin shugaban kasa a APC.

Jaridar The Cable ta ce Jakadan na Najeriya zuwa Benin ya bayyana zabinsa ne a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu 2022 da suka gana da ‘ya 'yan APC a Bauchi.

Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ya bayyana cewa yana goyon bayan Rotimi Amaechi domin tsohon Ministan shugaba ne da zai rike kowane kujera.

Kara karanta wannan

Takarar Amaechi ta na ta karfi, Buratai da tsohon IGP su na mara masa baya a zaben 2023

Tukur Buratai ya ce yana marawa takarar tsohon gwamnan Ribas baya ne saboda kwararren jagora ne shi, wanda zai dace da duk kujerar da ya dare kai.

Ofishin yada labaran takarar Amaechi ta rahoto jakadan yana yabawa ‘dan takarar na APC.

Janar Buratai ya na son Rotimi Amaechi
Rotimi Amaechi a Jigawa Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Za ku iya ji daga yadda aka gabatar da shi, an ji irin sanin aikin ‘dan takararmu. Mukaman da Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi abin burgewa ne.”
“Ya nuna cewa shi kwararren shugaba ne, jagoran da zai iya shiga ko ina, wanda ya iya kitsa dabaru, kuma ‘shi dan siyasa ne na bugawa a jarida.”

- Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya)

Buratai ya kara da cewa Rotimi Amaechi ya yi abin yabawa a duka wuraren da ya yi aiki a baya.

“A matsayin Shugaban majalisa, Gwamna, da kuma Minista, sannan lura da yadda ya rike shugaban kungiyar gwamnoni na kasa a lokacinsa.”

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi dalilan da suka sa ya fi kowa cancantar hawa kujerar Buhari a 2023

“Haka zalika abin da ya yi wajen jagorantar yakin neman zaben Muhammadu Buhari sau biyu. Wannan suka sa na ba shi cikakkiyar goyon-baya.”

Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya)

Kamar yadda jaridar ta rahoto, Buratai ya ce tsohon Ministan sufurin ya nuna kishi da kaunar Najeriya da rashin kabilaci, don haka yake ganin ya dace.

Alakar Amaechi da Buratai

A jiya kun ji labari cewa a lokacin da Tukur Buratai yake Birgediya Janar a gidan soja, shi ne ya jami'in da ya jagoranci rundunar 2 Brigade da ke jihar Ribas.

Shi kuma Rotimi Amaechi shi ne gwamna a wancan lokaci. Gwamnatin Amaechi ta ba Janar Buratai karfin gwiwar yakar tsagerun da suka addabi yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng