Takarar Amaechi ta na ta karfi, Buratai da tsohon IGP su na mara masa baya a zaben 2023
- Rotimi Amaechi yana cigaba da kokarin neman goyon bayan manya domin samun takara a APC
- Tsohon Ministan yana sha’awar zama ‘dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyya mai mulki
- Janar Tukur Yusuf Buratai da IGP Sulaiman Abba sun ni jirgin yakin neman zaben Amaechi a 2023
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jigawa - PM News a wani rahoto da ta fitar jiya, ta bayyana cewa tsohon shugaban hafsun sojojin kasa, Tukur Yusuf Buratai ya shiga tawagar Rotimi Amaechi.
Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya shi ne wanda ya rike hafsun sojojin Najeriya tsakanin 2015 da 2021, yana cikin hafsoshin da suka fi dadewa a bakin aiki.
Haka zalika tsohon shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya, Sulaiman Abba ya shiga jirgin Amaechi wanda yake harin tikitin shugaban Najeriya a APC.
Abba ya rike kujerar Sufetan ‘yan sanda na kasa ne tsakanin 2014 da 2015. Bayan Goodluck Jonathan ya fadi zabe, sai ya maye gurbinsa da Solomon Arase.
Tuni IGP Abba ya shiga siyasa, har ya nemi takarar Sanatan Jigawa a APC a zaben da ya wuce.
A gefe guda, Tukur Buratai yana cikin Jakadun da gwamnatin Muhammadu Buhari ta nada a shekarar 2021, tsohon sojan ne yake wakiltar Najeriya a Benin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton da mu ka samu ya ce tsofaffin jami’an tsaron su na cikin wadanda suka yi wa Amaechi rakiya da ya ziyarci jihar Jigawa domin ya gana da ‘ya ‘yan APC.
Alakar Amaechi da Buratai
Legit.ng Hausa ta fahimci Buratai yana cikin tawagar yakin neman zaben tsohon Ministan sufurin da ta yi zama da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kaduna.
A lokacin da Tukur Buratai yake Birgediya Janar a gidan soja, shi ne ya jagoranci rundunar 2 Brigade da ke jihar Ribas wajen kawo zaman lafiya a Neja Delta.
Bincike ya nuna mana Rotimi Amaechi shi ne gwamna a wancan lokaci. Gwamnatin Amaechi ta ba sojoji da sauran jami’an tsaro karfin gwiwar yakar tsageru.
Amaechi yana samun jama'a
Har ila yau Vanguard ta rahoto cewa kungiyar nan ta Fusion 774 ta dawo daga marawa Buratai takarar ya zama shugaban kasa, ta ce ta na tare da Amaechi.
Abin da ya kara nuna karin karbuwar tsohon Ministan shi ne an ji Gwamna Muhammad Badaru ya yi alkawarin ba zai yi takara a zaben fitar da gwani da shi ba.
Gwamnan na Jigawa ya ce ba zai iya adawa da tsohon Ministan sufuri watau Rotimi Amaechi ba saboda ubansu ɗaya a siyasa, don haka ne zai mara masa baya.
Asali: Legit.ng