2023: Ƴan Takara 3,000 Ne Za Su Fafata Don Neman Tikitin Takarar Majalisun Jihohi a APC

2023: Ƴan Takara 3,000 Ne Za Su Fafata Don Neman Tikitin Takarar Majalisun Jihohi a APC

  • Osita Okechukwu, Jigo a jam'iyyar APC ya ce yan takara 3000 ne ke neman kujerun majalisar jihohi a jam'iyyar gabanin 2023
  • Okechukwu ya sanar da hakan ne ranar Talata a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja wurin da za a yi aikin tantance yan takarar
  • Jigon na APC ya ce za su bi dokokin INEC, da na jam'iyyar APC da kundin tsarin mulkin Najeriya wurin tantance nagartattun yan takara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jigo a jam'iyyar APC, Osita Okechukwu, ya sanar a ranar Talata cewa yan takara 3000 ne za a tantance a fadin kasar da ke neman samun tikitin takarar majalisar jihohi gabanin zaben 2023.

The Punch ta rahoto cewa Okechukwu ya bayyana hakan ne dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja, wurin za a yi aikin tatance yan takarar majalisun jihohin.

Kara karanta wannan

Wakilan APC da PDP na ta jan miliyoyin kudi yayin da yan takara ke zawarcin kuri’unsu

2023: Ƴan Takara 3,000 Ne Za Su Fafata Don Neman Tikitin Takarar Majalisun Jihohi a APC
2023: Ƴan Takara 3,000 Ne Za Su Fafata Don Neman Tikitin Takarar Majalisun Jihohi a APC, Okechukwu. Hoto: VON.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce aikin tantance yan takarar zai zama ginshiki ne na gina sabbin shugabanni a kasar da za su fito daga jam'iyyun siyasa daban-daban, rahoton VON.

Ya ce:

"A bangarenmu a jam'iyyar All Progressives Congress, APC, za su tantance wadanda muke ganin sun cancanta yin takarar majalisun jiha.
"A siyasar Najeriya, mune kan gaba. Don haka muna da yan takara fiye da 3,000 a sassan kasar nan. Kuma muna son yin aiki mai kyau kuma mu saukaka wa masu zabe ta hanyar tsayar da yan takara masu nagarta da suka cika dukkan ka'idoji.
"Daya daga cikin ka'idojin shine kasancewa dan Najeriya, wanda ya kammala karatun sakandare kuma mai hali nagari. Wannan shine aikin mu. Muna aiki da ka'idojin INEC, da na jam'iyyar mu, APC da kundin tsarin mulkin Najeriya."

Tunda farko, Okechukwu ya ce APC za ta zabi sabbin deleget 44,045 da 2,322 domin fitar da yan takarar gwamna da shugaban kasa gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ta karewa Tinubu: Majiya ta ce APC ta gama zaban wanda zai gaji Buhari a 2023

2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa

A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.

Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.

Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.

A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164