Wakilan APC da PDP na ta jan miliyoyin kudi yayin da yan takara ke zawarcin kuri’unsu

Wakilan APC da PDP na ta jan miliyoyin kudi yayin da yan takara ke zawarcin kuri’unsu

  • Masu neman takarar kujerar shugaban kasa na ta kamun kafa a wajen wakilan jam'iyyunsu gabannin zaben fidda gwani
  • An tattaro cewa kasuwa ta budewa wakilan yayin da suke ta samun kyaututtuka musamman na kudi daga masu son mallakar tikitin manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu
  • Zuwa yanzu, akwai yan takara 38 da ke neman tikitin shugaban kasa, inda APC ke da 23, PDP kumu tana da mutum 15 a karkashinta

Yan takara 38 ne ke cikin tseren mallakar tikiti shugaban kasa a manyan jam’iyyun biyu. Yayinda APC ke da 23, PDP na da yan takara 15 da ke neman tikitin shugaban kasar ta.

Wakilan 7,800 a fadin kasar sune za su yanke makomar yan takarar APC 23 a tsakanin 30 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni.

A bangaren yan takarar PDP 15, wakilai 3,700 ne za su yi zabe don daukar mutum daya a tsakaninsu a matsayin wanda zai rike tutar jam’iyyar tsakanin 28 da 29 ga Mayu.

Kara karanta wannan

2023: Saura kwana 10 zabe, an shiga yamutsi a PDP game da wanda za a tsaida takara

Wakilan APC da PDP na ta jan miliyoyin kudi yayin da yan takara ke zawarcin kuri’unsu
Wakilan APC da PDP na ta jan miliyoyin kudi yayin da yan takara ke zawarcin kuri’unsu Hoto: Bukola Saraki
Asali: UGC

Kafin ainahin ranar, masu takarar shugaban kasar na ta zawarcin wakilan a jihohin su, suna gwangwaje su da kyaututtuka musamnan na kudi, yayin da suke kokarin tallata kansu, Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni daga jihohin sun nuna cewa wakilan na tara abun duniya daga yan takarar. Wani sashi na wakilan ya sanar da jaridar cewa watan yin kudinsu ne ya tsaya.

Daily Trust ta rahoto yadda barin dalar da yan takarar ke yi gabannin zaben fidda gwani ya ci gaba da fado da darajar naira.

Manyan yan takarar da ke yawon zawarcin wakilan APC a fadin kasar sun hada da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi.

A PDP, wadanda ke ta tunkarar wakilan daga wannan jihar zuwa wata sune Gwamna Nyesom Wike na Rivers, Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, Gwamna Bala Mohammed na Bauchi.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta jero sharudan da za su sa a hana mutum takara a 2023 bayan ya saye fam

Sauran sune Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom, tsohon shugaban majalisar defattaw Bukola Saraki, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Anambra, Pete Obi da shahararren dan kasuwa, Mohammed Hayatu-Deen.

Siyasar Najeriya: Alamu sun nuna Tinubu ya fi karbuwa a yankunan Arewa, inji majiya

A wani labarin, mun ji cewa babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, na ci gaba da samun garumin goyon baya a takararsa na son mallakar tikitin shugaban kasa na jam’iyya mai mulki.

PM News ta rahoto cewa wani bincike daga mabiya jam’iyyar a Kano, Kaduna, Katsina, Neja, Adamawa da wasu yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma ya nuna cewa babu wani dan takara da wakilai ke ganin mutuncinsa kuma suka yarda da shi kamar Tinubu.

Hakazalika shine ya samu tarba mai kyau sannan aka bayanna shi a matsayin jajirtaccen shugaba kuma dan jam’iyya na gaskiya.

Kara karanta wannan

APC da PDP sun fi karfin talaka da matasa: Adamu Garba ya sayi fom din takara a YPP

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng