Ta karewa Tinubu: Majiya ta ce APC ta gama zaban wanda zai gaji Buhari a 2023
- Akwai maganganun da ke cewa idan aka zo batun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, jam’iyyar karkata kallonta ga yankin Arewa maso Gabas
- Majiyoyin jam’iyyar APC da suka nemi a sakaya sunayensu na cewa jam’iyyar mai mulki na son mika tikitin mataimakin shugaban kasa a Kudu
- Idan har hakan ta tabbata, burin jiga-jigan masu neman shugabancin kasar nan da dama wanda a cikinsu akwai Bola Ahmed Tinubu zai zo karshe
Najeriya - Wasu majiyoyi daga jam’iyyar APC na luguden-lebe cewa shugabancin jam’iyyar na yin wani yunkuri na kule-kulle ta kasa na ganin yankin da za ta ba tikitin takarar shugaban kasa a 2023.
Majiyar ta ce, tuni dai APC ta fara shirye-shiryen mika tikitinta ga yankin Arewa maso Gabas, lamarin da ka iya ruguza begen Tinubu na gaje Buhari.
Daya daga cikin majiyoyin da suka yi magana da jaridar This Day a ranar Talata, 17 ga watan Mayu, ta ce da gaske APC na duba yadda a karshe za ta tantance shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin wanda zai tsaya takara a 2023.
Majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Abin da majalisar kasa ke kokarin yi shi ne ta mara wa Lawan baya da dimbin wakilai da aka kafa na ’yan majalisa na baya da na yanzu wadanda gyaran zai ba su damar halartar irin wadannan tarurruka.
"Suna cikin yanki mai kusan mutum 4,000, wanda da alama za su nuna goyon baya ga Lawan, don haka ne ma suke kokarin sake gyara dokar domin dacewa da son su da lissafinsu."
Batun tikitin mataimakin shugaban kasa
Ga tikitin mataimakin shugaban kasa, majiyar ta yi ikirarin cewa APC na duba ko dai ta tura shi ga Kudu maso Yamma ko kuma Kudu maso Kudu.
Wannan dai ya tabbatar da ikirari da Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto yayi na cewa jam'iyya mai mulki ta tsayar da Lawan a matsayin dan takararta na shugaban kasa.
Tambuwal, wanda dan takarar shugaban kasa ne na jam’iyyar PDP ne, ya bayyana cewa:
“Mun san dabararsu, suna son ganin sakamakon zaben fidda gwanin mu ya fito ne a ranakun 28 da 29 ga watan Mayu kafin su tantance wanda zai zama dan takararsu.
“Ku dubi shugaban jam’iyyar APC na kasa. Ya yi gum game da tsarin shiyyar da aka ce sun yi don kawai suna da shirin tsayar da Sanata Ahmad Lawan duba da wanene dan takarar shugaban kasa a jam’iyyarmu.”
Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar
A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman kujeran shugaba a 2023 karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya jaddada cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa a 2019.
Atiku yace kawai jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi amfani da karfin mulki wajen kwace nasarar daga hannunsa.
Ya kara da cewa sam ba zasu taba yarda a sake musu irin wannan a zaben 2023 idan jam'iyyar PDP ta bashi tikiti.
Asali: Legit.ng