Da Dumi-Dumi: An fara harbe-harben bindiga a Sakatariyar APC kan tantance yan takara

Da Dumi-Dumi: An fara harbe-harben bindiga a Sakatariyar APC kan tantance yan takara

Rivers - Karar tashin bindiga da zanga-zanga sun mamaye sakatariyar jam'iyyar APC da ke kan hanyar Woji a GRA, Patakwal babban birnin jihar Ribas yayin tantance yan takara.

Ɗaruruwan mambobin jam'iyyar da ke goyon bayan tsohon ɗan majalisar tarayya, Sanata Magnus Abe, ne suka mamaye wurin da nufin hana gudanar da tantance yan takarar majalisar jiha da zaɓen Deleget.

Tutar jam'iyyar APC.
Da Dumi-Dumi: An fara harbe-harben bindiga a Sakatariyar APC kan tantance yan takara Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Punch ta rahoto cewa fusatattun ƴaƴan jam'iyyar sun bayyana cewa sun isa wurin tun karfe 6:00 na safe amma sai suka taras an garkame kofa da kwaɗo.

Amma rikicin ya fara ne lokacin da wasu matasa suka yi yunkurin ɓalla kofar, hakan ya jawo hankalin jami'an yan sanda da aka girke a ciki suka fara harbin iska.

Ƙarar harbe-harben ya jefa tsoro da tashin hankali a zuƙatan mutanen da ke wurin, yayin da yan jarida da ke ɗaukar rahoton zanga-zangar suka fara gudun neman tsira da rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: EFCC Ta Kama Tsohuwar Kakakin Majalisar Najeriya, Patricia Etteh Kan Zargin Almundahar Miliyoyin Naira

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262